✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

City ta sayar wa Chelsea Cole Palmer, ta dauko Nunez daga Wolves

Palmer ya zura ƙwallo biyu a gasar cin kofin UEFA Super Cup da City ta doke Sevilla.

Chelsea ta sayi dan wasan gaban Ingila Cole Palmer daga Manchester City kan fam miliyan 40.

Yarjejeniyar ta haɗa da ƙarin fam miliyan 2.5 idan aka cika wasu sharudda kuma dan wasan mai shekara 21 ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru bakwai tare da zaɓin ƙarin shekara ɗaya.

Palmer yana cikin tawagar Ingila da ta lashe Gasar Cin Kofin Turai na ’yan ƙasa da shekara 21 a farkon wannan bazarar, kuma ya fara wasa ne a ɓangaren matasan City.

Palmer ya zura ƙwallo biyu a gasar cin kofin UEFA Super Cup da City ta doke Sevilla da kuma Community Shield da Arsenal ta doke su.

A baya, kocin City Pep Guardiola ya ce ba za a bar Palmer ya tafi aro ba. West Ham ta yi sha’awar sayen shi a farkon wannan bazarar amma ana tunanin tayin aro kungiyar ta yi.

Haka kuma, Manchester City ta kammala siyan dan wasan tsakiya Matheus Nunes daga Wolves kan fam miliyan 53.

Yarjejeniyar ta hada da batun bai wa Wolves kashi 10 cikin 100 daga duk wata ribar da City ta samu kan dan wasan mai shekaru 25 a nan gaba.

Dan wasan na Portugal, wanda ya buga wa kasarsa wasanni 11, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar da City.

Nunes bai halarci atisayen kungiyar ta Molineux a kwanan nan ba bayan ya bayyana cewa yana son komawa kungiyar Guardiola.

Wolves ta dauko Nunes kan kwantiragin shekaru biyar a bazarar da ta wuce, inda ta biya Sporting Lisbon fam miliyan 38.