Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta ce tana da karfin ikon rage kudin man fetur da ya yi tashin gwauron zabo a gidajen mai a fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Chinedu Okoronkwo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba.
- NAJERIYA A YAU – Shin Buhari Zai Iya Rayuwa A Daura?
- Dole mu hadu mu yaki talaucin da yake a Najeriya – Tinubu ga Gwamnoni
Okoronkwo ya bayyana cewa mambobinsa suna goyon bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi, kuma suna da kwarin gwiwa cewa hakan zai bude kofa ga masu zuba jari a harkar.
Shugaban na IPMAN ya kuma bayyana kwarin gwiwa cewa kungiyar na da karfin iko wajen rage farashin man fetur da zarar sun fara shigo da shi daga waje da kansu.
Tinubu a jawabinsa na farko a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, ya bayyana cewa an yi bankwana da biyan tallafin man fetur.
Sanarwar ta haifar da firgici, inda hakan ya haifar da karancin mai da hauhawar farashin man fetur.
Bayan sanarwar shugaban kasar, Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), ya sanar da kara farashin man fetur wanda a yanzu ana sayar da shi a kan N500 kan kowace lita daga N184 kowace lita a baya
Kungiyar kwadago ta nuna rashin amincewarta da cire tallafin man fetur tare da ganawa da wakilan gwamnati daban-daban.
Kotu ta dakatar da yajin aikin da kungiyar kwadago ta shirya shiga a ranar Laraba duk da cewa kungiyoyin sun ce sun dakatar da matakin.