Kwana hudu da fara binciken Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu amma Fadar Shugaban Kasa ba ta ce wa ‘yan Najeriya uffan a kai ba.
Hakan ya jefa ’yan kasar cikin lalube da rudani game da rahotannin dakatar da shi da kuma nada wanda aka ce zai rike hukumar.
Shirun gwamnatin kan binciken ya dami ‘yan kasar, musamman kasancewar jagoran yaki da cin hanci da rashawa a gwamanatin Shugaba Buhari, shi ake bincika.
Babu masaniya a kan Kwamitin Salami
Hasali ma, mutane ba su da masaniya kan kwamitin tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Najeriya, Ayo Salami wanda aka ce Shugaba Buhari ya kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Magun.
Har wa yau, fahimtar inda kwamitin ya dosa da wa’adinsa na binciken Magu wani abu ne a lullube.
Sai dai wata majiya ta ce, kwamitin ya dade yana binciken wasu tarin takardu tare da ganawa da wasu mutane kafin ya gayyaci Magu ya amsa tambayoyi.
An ce Buhari ya kafa kwamitin ne domin cin ta bakin Magu a kan takardar zargin rashawa da Ministan Shari’a, Abubakar Malami a gabatar wa shugaban a kan sa.
Sai dai a ranar da Magu ya bayyana a gaban kwamitin, dirar mikiya jami’an taron DSS suka yi masa, watau ba a gudanar da abun yadda ake ganin tsarin aikin gwamnati ya tanda ba.
Amma Mai Magana da yawun Shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce ba kama shi aka yi ba, gayyatarsa aka yi.
Shi ma Kakakin Ministan Shari’a, Umar Gwandu ya ce ba shi da masaniya kan kamun da aka yi wa shugaban na EFCC.
“Yanzu ku ke sanar da ni, ba ni da masaniya kan wata takardar rashawa da aka ce maigidana ya rubuta a kan Magu”.
Rudani a ofishin EFCC
A daren ranar Talata Kamfanin Dillacin Labarai na NAN ya rawaito cewa Mohammed Umar, wanda Mataimakin Kwamishinan ’Yansanda ne kuma Daraktan Gudanarwa a EFCC shi aka ba wa rikon kwaryar hukumar.
Rahoton ya ce ma’aikatan hukumar ne suka zabe shi, sai dai kuma har yanzu ba a rubuto wa hukumar cewar an dakatar da Magu ba.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin EFCC, amma bai ce uffan ba kuma duk kokarin Aminiya na binciko abin da ke faruwa ya ci tura.
Fadar shugaban kasa ta yi gum
Haka nan kuma duk kokarin Aminiya na ji daga bakin fadar shugaban kasa bai yi nasara ba.
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu, bai ce komai ba.
Da ya tuntubi Ministan Watsa Labarai, Lai Mohammed, sai ya ce ba huruminsa ba ne ya amsa tambaya kan Magu, amma ya tambayi Ministan Shari’a.
A jiya Aminiya ta yi rahoto game da wasu mutum hudu da ake tsammani za su maye gurbi Magu.
Daga cikinsu akwai tsohon Mataimakin Sufeto Janar na yansanda Mohammed Sani Usman da Kwamishinan Yansanda na Abuja, Bala Ciroma.
Akwai kuma Tsohon Mataimakin Sufeto Jamar na ‘Yan Sanda daga Kebbi da Kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Enugu, Ahmad Abdurrahman.
Sai dai wasu gidajen jarida (ba Aminiya ba) usn sun rawaito cewar an riga an zabi Ciroma amma Rundunar ‘Yan Sanda ta Abuja ta ce ba ta san da maganar ba.
An bar ’Yan Najeriya cikin duhu
Auwal Musa Rafsanjani, wanda shi ne Darektan Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) ya koka bisa yadda Gwamnatin Tarayya ta bar mutane cikin duhu a kan binciken Magu.
Rafsanjani, a hirar da ya yi da wakilinmu ya ce, idan ba a bi sannu ba, binciken zai iya zubar da kimar Najeriya a kan kokarinta na yakar cin hanci da rashawa a idon duniya.