Cinikin makamai na karuwa a nahiyar Turai a cewar Cibiyar SIPRI da ke bincike kan zaman lafiya da yaduwar makaman nukiliya a duniya.
Hakan na kunshe cikin alkaluman da cibiyar ta sanar a wannan mako wanda daya daga cikin mawallafan binciken, Pieter Wezeman, ya bayyana a matsayin babbar damuwa.
- Wata Sabuwa: An kori Sakataren APC na Kasa
- Taraba: ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace mai gari da matansa
Sai dai Ian Anthony, Daraktan Tsaro na Turai a Cibiyar SIPRI, ya ba da rahoton cewar cinikin makamai a duniya ya ragu kadan a cikin ’yan shekarun nan.
Cinikin makaman kamar tankunan yaki da jiragen yaki da na ruwa na karkashin teku ya ragu da kashi 4.6 cikin 100, daga shekara ta 2017 zuwa 2021 idan aka kwatanta da shekaru biyar da suka gabata.
A rahoton da ta bayyana na shekara, cibiyar binciken zaman lafiya ta SIPRI da ke birnin Stockholm ta ce a Turai cinikin makaman ya karu da kashi 19 cikin dari.
Sai dai alkalluman ba su tabo batun yakin da ake yi ba a Ukraine a game da makaman da ake shigar da su a kasar.
Kidididgar ta nuna cewa manyan masu shigo da makamai a Turai su ne Birtaniya, Norway da kuma Netherlands.
Ana kuma sa ran sauran kasashen na Turai za su kara yawan makaman da suke shigarwa kasashensu nan da shekaru goma masu zuwa, musamman yadda a baya bayan nan suka mika bukatar shigo da jiragen yaki da Amurka.
A cewar Pieter D. Wezeman, daya daga cikin manyan masu bincike kan yaduwar makamai a cibiyar SIPRI, tabarbarewar dangartaka tsakanin yawancin kasashen Turai da Rasha a bayan nan ce ta ta’azzara yunkurin shigo da makaman musamman a tsakanin kasashen da ke da karancin masana’antun kera makamai.