Mawaƙi Malam Usman Mai Dubun Isa da ake tuhuma da cin zarafin Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari da Sheikh Ibrahim Inyass ya janye kalamansa.
Mai Dubun Isa wanda ke kotun Musulunci dake PRP Gama a jihar Kano ta tura shi zaman waƙafi ya bayyana tubansa ne da a zaman kotun da aka gudanar ranar Laraba.
Ya ce “Mun janye wannan magana ta kama suna da kuma nuna hoto, kuma nan gaba duk wanda abin ya ɓata wa muna ba shi haƙuri akan manufarmu ke nan don mu ɓata wa al’umma ba.”
Kotun Musulunci ta tsare mawaki ‘Mai Dubun Isa’ a gidan yari
Abba ya nada Sheikh Daurawa shugabancin hukumar Hisbah ta Kano
A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da ƙara Malam Muhammad Al-Bakri Mika’il ya ce sun amince su karbi tubansa bisa sharaɗai guda uku.
Muhammad Al-Bakri Mika’il ya ce sharaɗan sun haɗa da janye kalamansa, bada haƙuri ga iyalai da mabiyan malaman, da kuma alƙawarin ba zai sake wata magana game da ɗariƙar Tijjaniyya ba.
Ya ce “Ba kes muka kashe ba, mun rataye kes ne da sharuɗa, in ya ci gaba da biyayyar sharuɗa to kes ya na nan a rataye.
“Idan kuma ya karya ɗaya daga cikin sharuɗan to za a komo ruwa.