✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya nada Sheikh Daurawa shugabancin hukumar Hisbah ta Kano

A baya dama ya taba rike hukumar har sau biyu

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shugabancin Hukumar Hisbah ta Jihar.

A baya dai, Sheikh Daurawa ya taba jagorantar hukumar har sau biyu, a zamanin mulkin tsohon Gwamnan Jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma farkon mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai a shekara ta 2018, Daurawa ya sanar da ajiye mukamin lokacin da aka samu sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Amma a ranar Litinin, malamin ya wallafa wani bidiyo da ya nuna shi yana karbar takardar sake nada shi shugabancin hukumar a karo na uku, daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Baffa Abdullahi Bichi.

Ana ganin malamin ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gwamnatin Jihar mai ci ta jam’iyyar NNPP.