Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Ina mai shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kadai Yake, ba Ya da abokin tarayya. Ina mai shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawanSa ne, kuma ManzonSa.
Ya bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah matukar jin tsoronSa, kada ku mutu sai kuna Musulmi. Ku sani cewa, Allah (SWT) Ya sanya alaka mai karfi a tsakanin Musulmi da Musulmi, fiye da alaka ta ’yan uwantaka.
Allah (SWT) Ya ce: (Ku sani) “Muminai ’yan uwan juna ne. Ku kyautata ’yan uwantakarku……” Suratul Hujurat (10).
Allah (SWT) Ya ce: “Wadanda ke cutar da muminai maza da mata a kan abin da ba su aikata ba, lallai sun dauki (zunubin) kirkira (ta karya) da zunubi mabayyani.” Ahzab 58.
Don Allah ku karanta, akalla Suratul Ahzab da Nur da Hujurat ku ji abin da Allah Ya fada game da matsayin Musulmi da hukuncin wanda ya ci mutuncinsa.
Nu’uman Bn Bashir (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Misalin muminai wajen nuna kauna da tausaya wa junansu, kamar gangar jiki (daya) ne, idan wata gaba tana rashin lafiya, duk sauran sassan jiki sai su taya ta jin radadin da zazzabin.” Bukhari da Muslim
A wani Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Mumini da mumini kamar tubalin gini ne ga daya tubalin. Daya na haduwa da daya (su karfafa juna).” Bukhari da Muslim
Wannan babban misali ne. Idan aka jera bulo 100 na gini aka hade tsakaninsu, aka shafe su da siminti sai su koma kamar bulo daya. Allahu Akbar!
Hakkin Musulmi a kan Musulmi
Annabi (SAW) ya ce: “Hakkin Musulmi a kan Musulmi (guda) shida ne:
- Ka amsa sallamarsa
- Idan ya gayyace ka ka amsa
- Idan ya nemi nasiharka (shawararka) ka yi masa (kamar yadda za ka yi wa kanka)
- Idan ya yi atishawa ya yi godiya ka yi masa addu’a
- Idan ya yi rashin lafiya ka ziyarce shi
- Idan ya rasu ka bi gawarsa. (Muslim ya ruwaito).
Haramcin kaurace wa juna
Musulunci ya hana Musulmi ya kaurace wa dan uwansa Musulmi su daina magana da juna har sama da kwana uku.
Abu Huraira (RA) Ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Ana bude kofofin Aljanna duk Litinin da Alhamis. Kuma ana gafarta wa duk wani bawan da ba ya shirka da Allah. Sai dai mutumin da ke da sabani da dan uwansa (Musulmi, ba su magana da juna), sai a ce ku jinkirta wa wadannan har sai sun sasanta, sai a ce ku jinkirta wa wadannan har sai sun sasanta.” Muslim
A wani Hadisi na Abu Huraira (RA) ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Bai halatta ga Musulmi ya kaurace wa dan uwansa (Musulmi) ba sama da kwana uku, duk wanda ya kaurace (wa dan uwansa Musulmi) sama da kwana uku ya mutu (a wannan hali) zai shiga wuta.” Abu Dawud
Wajibcin nuna kauna ga Musulmi
Anas (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Dayanku ba zai zama mai imani ba, har sai ya so wa dan uwansa abin da yake so ga kansa.” Bukhari da Muslim.
A wani Hadisi na Abu Huraira (RA): Annabi (SAW) ya ce: “Ba za ku shiga Aljanna ba, har sai kuna da imani. Ba za ku samu imani ba kuwa, har sai kuna kaunar junanku. In fada muku abin da za ku rika yi, kauna ta shiga tsakaninku? Ku rika yada sallama a tsakaninku.” Muslim.
Wajibcin kame harshe daga cin mutuncin Musulmi da yin magana game da shi a bayan idonsa
Mu’azu dan Jabal (RA) ya ce da Annabi (SAW): “Ya Ma’aikin Allah! Nuna mini wani aiki da zan yi wanda zai shigar da ni Aljanna, ya nesanta ni daga wuta. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Lallai ka tambayi babban al’amari, amma yana da sauki ga wanda Allah Ya saukaka mawa! Bayan ya fada masa shika-shikan Musulunci biyar da yin sadaka da sallar dare da jihadi, sai ya ce, in fada maka abin da zai kubutar da wadannan gaba daya? (Ko ya rusa su?). Sai ya kama harcensa, ya ce: ‘Ka kiyayi wannan! Sai mu’azu ya ce: “Ashe duk abinda muke fada ana hukunta mu a kansa? Sai Annabi (SAW) ya ce: “menene (yawancin) abin da yake jefa mutane a wuta a kan fuskokinsu in ba abubuwan da harasansu ke furtawa ba?” Tirmizi.
A wani Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Ya ishi mutum sharri (zunubi) ya tozarta dan uwansa Musulmi. Haramun ne a kan kowane Musulmi ya keta wa dan uwansa Musulmi, (zubar da) jininsa da (cin) dukiyarsa da (zubar da) mutuncinsa.” Muslim
Allah (SWT) ya ce: “Duk wanda ya kashe mumini da gangan, sakamakonsa Jahannama, zai dawwama a ciki. Allah Ya yi fushi da shi, kuma Ya la’ance shi, kuma Ya tanadar masa azaba mai girma.” Suratun Nisa’i: 93
Abu Huraira (RA) Ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Mutum uku, ni zan yi rigima da su (a gaban Allah) Ranar Kiyama. Daga cikinsu akwai wanda ya sayar da mutum mai ’yanci ya ci kudin…….” Bukhari
Game da cin dukiyar Musulmi da zalunci kuwa Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yanki hakkin wani Musulmi da damarsa (hannunsa) Allah Ya wajabta masa shiga wuta, kuma Ya haramta masa shiga Aljanna.” Sai wani mutum ya ce: Koda karamin abu ne? Annabi (SAW) ya ce: Koda kamar girman ashuwaki ne.” Muslim
Haramcin sakin baki
Allah (SWT) Ya ce: “(Mutum) Ba ya furta wata magana illa akwai mai lura (rubutawa) halartacce.” Ma’ana yana tare da shi kowane lokaci. Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Allah Ya fadi alheri, ko ya yi shiru.” Bukhari da Muslim
Abu Musa Al’Ash’ariy (RA) ya ce: “Na ce ya Ma’aikin Allah! Wane ne mafifici a cikin Musulmi? Sai ya ce: (Shi ne) “Wanda Musulmi suka kubuta daga (sharrin) harcensa da hannayensa.” Bukhari da Muslim
A Hadisin Sahal, ya ce: Annabi (SAW) ya ce: “Wane ne zai lamunce (tsare) mini abin da ke tsakanin lebbansa (harcensa) da abin da ke tsakanin kafafunsa (farjinsa), ni kuma in lamunce masa shiga Aljanna?” Bukhari da Muslim
Ya bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah ku tsare mutuncin junanku, ku tsare harasanku, mutum ya zauna ya yi ta zuba (ko rubuta) magana ba lissafi, yana da hadari kwarai da gaske.
Annabi (SAW) ya ce: “Bawa yakan furta wata kalma da Allah Yake so, bai dauke ta a bakin komai ba. Amma Allah Ya daukaka shi zuwa ga wani matsayi, saboda ita. Kuma bawa yakan furta wata kalma da Allah ba Ya so, shi bai dauke ta a bakin komai ba, amma ta jefa shi a Jahannama ya yi ta gangarawa a cikinta.” Bukhari
Zagin Musulmi haramun ne
Abdullahi dan Mas’ud (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Zagin Musulmi fasikanci ne, yakarsa (kashe shi) kuwa kafirci ne.” Bukhari da Muslim
A’isha (RA) ta ruwaito cewa Annabi (SAW) yana cewa: “Kada ku zagi wadanda suka mutu, sun riga sun tafi ga abin da suka aikata.” Bukhari
Ya ’yan uwa masu girma! Abin da muke gani a kwanan nan na zagi da cin mutuncin mutane a soshiyial midiya (kafafen sadarwar zamani) musamman malamai da shugabanni har da wadanda suka mutu ba zai yi wa duk wani mai hankali da ya san addini dadi ba. A matsayinmu na Musulmi da muka yi imani da Allah, muka yarda da hisabi. Mu ne kuma muke keta dokokin Allah, muke cin mutuncin junanmu. Abin mamaki wadanda ba Musulmi ba a kasar nan ba mu ganin suna haka. Nasu ko ya yi laifi, ya yi barna, ba za su fito su tozarta shi a duniya ba.
Haramcin bin sirrin Musulmi
Abu Huraira (RA) Ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Ina yi muku gargadi game da zato, domin zato karyar zance ne. (Ma’ana kada ka yi wa dan uwanka mummunan zato, ba tare da samun hujja na tabbacin ya aikata ba, ka tabbatar masa da laifi). Kada ku kasa kunne (don jin aibin mutum), kada ku bi (diddigi) sirrin juna, kada ku yi gasa, kada ku yi wa juna hassada, kada ku kyamaci junanku, kada ku juya wa juna baya (gaba) ku zama bayin Allah ’yan uwan juna, kamar yadda Allah Ya umarce ku. Musulmi dan uwan Musulmi ne, kada ya cuce shi, kada ya wulakanta shi, kada ya kaskanta shi, tsoron Allah a nan (zuci) yake……. Allah ba Ya duban (kyawun) jikinku, ko kirarku, amma abin da yake dubawa shi ne zukatanku da ayyukanku.” Muslim
Mu’awiya dan Abu Sufyan (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Idan ka ce za ka bi diddigin (sirrin) Musulmi, za ka bata (kushe) su. (domin babu wanda ba ya da laifi).” Abu Dawud
Allah (SWT) Ya daukaka Musulunci da Musulmi, Ya ba mu ikon ganin mutuncin junanmu, amin!