Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Mugunguna ta Kasa (NAFDAC) ta yi gargadin cewa masu cin kayan marmarin da aka nika su da sinadarin Calcium Carbide da cewa za su iya kamuwa da cututtuka kamar Kansa
A cewar hukumar, sinadarin, wanda galibi ’yan kasuwa ke amfani da shi wajen nikon, domin kayan su nuna da wuri, na dauke da guba.
- Ba mu da shirin sake kara farashin man fetur a yanzu – Tinubu
- Kenya ta dawo da tallafin mai bayan fuskantar matsin lambar jama’a
Ko-odinetar hukumar a Jihar Bauchi, Josephine Abbas Daylim, ce ta yi wannan gargadi ranar Talata a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya na yankin Arewa maso Gabas.
Josephine ta ce an jima ana samun rahoton masu sanya gubar wajen nika danyen mangwaro ko ayaba da aka tsinko daga jikin bishiyarsa yana danye domin ya nuna da wuri, na da matukar illa.
Ta kuma koka kan yadda ta ce ana tallan magunguna a kwando a cikin rana, duk da cewa dama ba su da lasisi ko kwarewa wajen sayar da maganin a kan titi.
Sai dai jami’ar ta ce hukumar ba za ta iya shiga kowanne lungu da sako ba, dalili ke nan ma da shigo da jami’an tsaro da ’yan jarida domin su taya ta aikin.
Daga nan sai ta yi kira ga al’umma da su guji sayen irin wadannan kayayyakin domin su zauna lafiya.