Kungiyar Ma’aikatan Majalisun Dokokin Jihohi ta kasa Parliamentary staff Association of Nigeria (PASAN) a ranar Litinin ta rufe Majalisar Dokokin Jihar Gombe saboda bin umurnin uwar kungiyar a faɗin Najeriya.
Shugabanin kungiyar sun rufe Majalisar ne biyo bayan umurin da aka basu saboda gaza cika umurnin da gwamnati ta bayar a baya na bai wa Majalisun Dokokin ’yancin cin gashin kai a harkokin gudanarwarsu.
- Ya kamata Najeriya ta fara tsarin mulki na shekara 6, babu tazarce
- Mun gano gawarwaki 80 a maboyar masu garkuwa da mutane – Gwamnan Abiya
Da yake zantawa da manema labarai a Gombe, shugaban kungiyar Muhammad Bello Dukku, cewa ya yi sun dauki matakin rufe Majalisar ne saboda kunnen kashi da gwamnatin jihar ta yi na kin cika umurnin gwamnatin tarayya na bai wa Majalisun Dokoki ’yancin cin gashin kai.
Muhammad Bello Dukku, ya kara da cewa Majalisar za ta ci gaba da zama a rufe har sai baba-ta-gani kuma sun umurci daukacin ma’aikatan majalisar da su ci gaba da zama a gida.
Shi ma Sakataren Kungiyar Aminu Aliyu, ya ce rufe Majalisar cika umarnin uwar kungiyar ne la’akari da rashin samun ’yancin cin gashin kai wajen gudanar da harkokin kudi kamar yadda wata doka da tsohon Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya shigar cikin doka.
Ya ce majalisun za su ci gaba da kasancewa a rufe faɗin Najeriya duk da cewa an yi ta gudanar da tarurrukan cimma matsaya amma hakan bai haifar da da mai ido ba.
Wani mamba kuma daya daga cikin Ma’aikatan Majalisar da wakilinmu ya zanta da shi, Solomon Livinus ya ce suna goyon bayan kungiyar ta su duk da cewa ana teburin tattaunawa amma dai za su ci gaba da zama a gida har sai yadda hali ya yi.
Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin rufe majalisar ma’aikatan sun yi zanga-zangar lumana rike da kwalaye masu dauke da sakonni daban-daban na neman ’yanci.