HOTUNA: Yadda Sallar Idi ta gudana a sassan Najeriya
Galibin al’ummar Musulmi a Najeriya sun bi sahun takwarorinsu na sassan duniya wajen bikin Karamar Sallah ranar Lahadi. Ko da yake an samu wadanda suka…
DagaSani Ibrahim Paki
Sun, 24 May 2020 12:58:50 GMT+0100
Galibin al’ummar Musulmi a Najeriya sun bi sahun takwarorinsu na sassan duniya wajen bikin Karamar Sallah ranar Lahadi.
Ko da yake an samu wadanda suka yi tasu sallar ranar Asabar – wasu ma tun ranar Juma’a suka yi – suna masu cewa sun ga wata.
Ga dai hotunan yadda Sallar ta gudana a wasu wurare.
Masallacin Isyaka Rabi’u da ke Gwauron Dutse, Kano.Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yayin Sallar a babban filin Idi na KanoGwamna Ganduje, Sarkin Kano tare da wasu mukarrabansu a filin Sallar Idi a KanoShugaba Buhari da iyalensa sun gudanar da Sallar a Fadar Shugaban KasaUwar gidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari tare da sauran iyalanta lokacin Sallar Idin a fadar shugaban kasa.Shugaba Buhari tare da iyalansa suna daukar selfie.
Sallar Idi a Masallacin Shehu Karami, da ke Tudun Yola, Kano.Masallacin Hotoro, KanoDokar kulle ta sa wasu mazauna Abuja tafiya har Jihar Nassarawa domin samun halartar sallar Idin.Wasu mazauna yankunan Abuja da suka ketara zuwa jihar Nasarawa don yin Sallah Idi ranar Lahadi.Masallacin Zam-Zam, Hotoro Tsamiyar Boka a Kano