CIKIN HOTUNA: Irin barnar da fashewar ammonium ta yi a Lebanon
Sama da mutum 100 ne suka mutu yayin da dubbai suka jikkata a Beirut babban birnin Lebonon, bayan wata mummunar fashewa. A wani rahoto da…
Helikwaftan sojoji yana feshi domin kashe wutar da ke ci har safiyar Laraba 5 ga Agusta, 2020
DagaJamilu Adamu
Wed, 5 Aug 2020 16:43:02 GMT+0100
Sama da mutum 100 ne suka mutu yayin da dubbai suka jikkata a Beirut babban birnin Lebonon, bayan wata mummunar fashewa.
A wani rahoto da BBC ta wallafa na cewa, Shugaban kasar Michel Aoun ya ce ton fiye da 2,750 na sinadirin Ammonium nitrate da aka ajiye a wata ma’adana na shekaru shida ne ya janwo wannan barna.
Masu aikin ceto na kokarin gano wadanda suka makale a wurin da abin ya faru.Sojoji sun hako wani mutum da ya makale a karkashin gini. Hoto: AFP.Jirgin sojin Lebanon na shawagin duba irin barnar da ta faru. Hoto: Reuters.Wani mutum yana duba barnar da lamarin ya yi a wani gida a Beirut. Hoto: Reuters.Gabar teku a a Beirut inda aka samu fashewar sunadarin na Ammonium nitrate.Wasu jiragen ruwa ke ci da wuta a gefan teku da ke BeirutWani bangare na Beirut inda fashewar ammonium nitrate ta shafa. Hoto: AFPYadda lamarin na ranar Talata ya yi barna a assa na birnin Beirut. Hoto: AFP.Yadda wasu gine-gine suka rushe bayan fashewar sunadarin a Beirut. Hoto: AFP.