Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta mika sunan wani jigon dan siyasa daga Jihar Katsina, Alhaji Kabiru Ibrahim Masari a matsayin wanda zai yi wa Asiwaju Bola Tinubu abokin takarar Shugaban Kasa na wucin gadi.
Wannan dai na zuwa ne a sakamakon rashin cimma matsaya da jam’iyyar APC ta yi bayan cikar wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayar na mika sunayen ‘yan takarar kujerar Mataimakin Shugaban Kasa.
An mika sunan Masarin bayan yarjejeniyar da aka yi da shi na cewa zai janye daga matsayin mataimakin bayan an cinma matsaya kan wanda ya kamata ya zama mataimakin dan takarar kamar yadda a sashe na 31 na Dokar zabe ya sahale.
A ranar Juma’a ce dai wa’adin da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayar na mika sunayen ‘yan takarar kujerar shugaban kasa.
“An zabe shi a matsayin mataimakin na wucin gadi har zuwa lokacin da za a warware wasu batutuwa a kan abokin takarar,” kamar yadda wani daga cikin yaran Tinubu Bola Tinubu ya shaidawa Aminiya.
“Tinubu yana ci gaba da tuntubar mutane kan zaben abokin takararsa. Zai maye gurbin Masari da zarar an zabi wanda ya dace,” inji wata majiya.
Sashe na 31 na Dokar Zaben cewa ya yi: “Dan takara na iya janye takararsa ta hanyar sanarwa a rubuce wacce ya sanya wa hannu sannan kuma ya mika ta ga jam’iyyar siyasar da ta tsayar da shi takara. Ita kuma jam’iyyar ta gabatar da haka kafin kwanaki 90 zuwa gudanar da zabe.”
Alhaji Kabiru Ibrahim Masari, wanda ya kasance tsohon Sakataren Kula da Walwalar Jama’a na jam’iyyar APC na Kasa a zamanin Kwamared Adams Oshiomhole, ya fito ne daga kauyen Masari da ke Karamar Hukumar Kafur a Jihar Katsina.
A baya kafin kafuwar jam’iyyar APC, Masari ya kasance dan jam’iyyar PDP a zamanin tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Umaru Musa Yar’adua.
Bayan rasuwar Yar’adua a shekarar 2010, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Congress for Progressives Change (CPC) jam’iyyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi takara a karkashinta amma ya fadi zaben 2011, wadda kuma gabanin zaben 2015, CPC ta rikide tare da wasu jam’iyyun zuwa APC.
A baya dai, akwai rade-radin cewar an mika sunayen tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima da Gwamna Babagana Zulum (Borno) da Abdullahi Umar Ganduje (Kano) da Atiku Bagudu (Kebbi) da Muhammad Abubakar Badaru (Jigawa) da Nasiru El-Rufai (Kaduna) da kuma Simon Bako Lalong (Filato) a matsayin wadanda a cikinsu ne daya zai zamo mataimakin Tinubun a zabe mai zuwa.