A ranar Lahadin da ya gabata ne ya zama ranar tunawa da samun ‘yancin kan Najeriya shekaru 57 tun bayan da turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mika mulkin a shekarar 1960. Wasu yankunan kasar sun shafe shekaru masu yawa karkashin ikon turawan gabanin kafa kasar a shekarar 1914. Koda yake a wancan lokacin muna da dauloli da masarautu da sauran gundumomi daban-daban kafin zuwan turawan, amma hakan bai sa mun hade mun zama kasa guda ba har sai bayan zuwan turawan.
An yi wannan biki ne sama-sama daga dukkan bangarorin gwamnatin uku da ake da su, kila saboda raunin tattalin arzikin kasar, ko kuma saboda rashin cikakken tsaro dake addabar kasar daga dukkan yankunan kasar ko kuma saboda kasancewar shekaru 57 ba su da cikakken kima kamar 10 da 25 da 50 ko 100.
Duk da cewa an shafe fiye da shekaru 100 da kirkirar kasar, sannan kuma ta shekara 57 da samun ‘yancin kai, wasu al’ummar kasar ba su gamsu da tafarkin da kasar ta sa gaba ba. Wasu al’ummar na kokawa game da yadda suke ganin an maida su saniyar ware. Yayin da wasu ke hankoran neman a sake fasalin kasar baki daya. Wasu kuma na dora alhakin tabarbarewar tattalin arzikin kasa da rashin walwala da kuma yawaitar ayyukan rashawa kacokam ga shugabannin siyasa. Haka nan wasu na son ballewa sun kafa wata kasar daban, yayin da kuma kungiyar Bokom Haram ta kaddamar da yaki da nufin rushe gwamnatin kasar. A waje da siyasa kuma, gungun miyagu na kara taimakawa wajen durkusar da kasar ta hanyar yawaitar garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma fashi da makami. Wannan fa duka na faruwa ne a lokacin da kasar ke kokarin farfadowa daga rugujewar tattalin arziki.
Wadannan dalilai a sarari sun isa su nuna rashin muhimmancin shirya bukukuwan tunawa da ranar, koda yake halin da kasar ke ciki a yanzu ba mai kyau ba ne, amma dole ne mu tuna cewa wannan kasa fa ta tsallake manyan rigingimu a baya wadanda suka fi karfin wadanda mu ke ciki yanzu. Ciki kuwa har da hargitsewar juye-juyen gwamnatoci guda shida bi-da-bi, da manya-manyan tawayen jama’a, da hare-haren kungiyoyi sannan da kuma yakin basasa wanda ya lashe rayuka sama da miliyan guda. Amma babban abin takaicin shi ne yadda wasu kara ruruta wutar fitintinu tamkar babu wani darasi da muka koya a baya. Wasu daga cikin jigogi tare da magoya bayansu masu karancin ilimi na son hargitsa kasar saboda cimma wasu muradun kashin kai da kabilanci marsa kan gado wadanda aka gina kan rahotannin karya. Domin wadanda ke kukan cewan an maida su saniyar ware, sun yi fintikau ta fuskar cigaban rayuwa da walwalar jama’a fiye da sassan da suke zargi da nuna bambancin a gare su.
Domin ciyar da Najeriya gaba, ya kamata kowane dan kasa ya tabbatar da cewa akwai gudumawar da yake bayar wa wajen gina wa tare da wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasa. Muddin babu zaman lafiya, to babu cigaba kamar yadda muke gani a Sudan ta Kudu da Siriya da Afganistan da Iraki da Libiya da Yemen da sauransu. Garuruwa sun ruguje tsawon lokaci saboda son zuciya kamar yadda ya faru Libiya; Yamen ta shiga rudani sakamakon tawaye da kwadayin mulki; ko kuma saboda rashin hakuri da kuma muguwar adawa wadda ya haddasa yake-yake a Siriya.
A Najeriya kuma, wasu daga cikin masu fafituka na tabbatar mana da cewa a shirye suke da su dulmiyar da kasar tare da sabawa dokokin kasar don cimma miyagun bakatunsu. Idan da gaske mun yarda da tsarin dimokuradiyyarmuwajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci da wanzar da zaman lafiya, to ashe kenan dukkan wanda ke da korafi a Najeriya ya hanyoyin doka da tsarin da dimokuradiyyar ta shimfida don cimma nasara. Babban abin buga misali shi ne Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya lashe zabe bayan da ya sha kaye sau uku a jere, lamarin dake nuni da hakuri da kuma bin doka da oda.
Don haka a wannan gabar muke kira ga dukkan al’ummar kasar nan maza da mata cewa, su yi watsi da tunanin cewa komai ya rataya ne ga gwamnatin tarayya. E hakika gwamnatin tsakiya ta na da hurumi wajen kula da al’amuran da bai fi karfin ikonta ba. Amma fa kusan rabin kudaden shigar dab gwamnati ke samu na tafiya ne zuwa jihohi da kananan hukumomi. Idan da za su aiwatar da wadannan kudade yadda ya kamata, to da al’amura sun daidaita fiye da yadda suke a yanzu. Amma duk da haka wasu sun kawar da kai ga irin facakar da jihohinsu ke yi wanda suka hana al’amura tafiya yadda suka kamata, suna neman ballewa daga kasar baki daya. To lokaci ya yi da zamu canja tubnaninmu don fuskantar zahiri.
Koda yake muna farin ciki da yadda ake yakar cin hanci da rashawa, wadda dukkan gwararru suka yarda cewa yana taimakawa wajen farfado da tattalin arziki da harkokin raya kasa, wadda kuma shi ne babban manufar wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari. Kuma wannan yaki da ake da rashawa ya dan ci karo da ‘yar tangarda bisa wasu dalilai. Wadanda suka hada da raunin bincike da gurfanarwa, da kuma baragurbin masu shari’a da kuma yadda gwamnatin ke kau da kai ga makusantanta, wadannan kurakurai na bukatar gyara kafin a samu cikakken nasarar da za ta aza kasar bisa kyakkyawan tafarki.