’Yan Najeriya sun ce babu abin da suka fi bukata daga gwamnatin kasar kamar ta samar musu da cikakken tsaro tare da sauran romon dimokuradiyya.
’Yan kasar sun jaddada bukatar gwamnatin ta ba da cikakken muhimmanci ga sha’anin tsaron rayuka da dukiyoyi, domin a cewarsu, yadda matsalar tsaro ke kara kamari a kasar ya sa ba su da kwarin gwiwa a kan gwamnati.
- NAJERIYA A YAU: Shekara 23 Da Mulkin Dimokuradiyya: Ina Aka Kwana?
- Barcelona za ta kece raini da Madrid da Juventus a wasannin sada zumunta
Sun bayyana haka ne a daidai lokacin da kasar ta yi bikin zagayowar Ranar Dimokuradiyya ta 2022 a ranar Lahadi.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara domin tunawa da zaben da aka gudanar a makamanciyar ranar a shekarar 1993.
Marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola na jam’iyyar SDP ne ya lashe zaben, amma gwamnatin sojin lokacin, wadda Janar Ibrahim Badamasi Babangida ke jagoranta ta soke zaben.
Ana ganin zaben na ranar 12 ga watan Yuni, 1993 a matsayin sahihin zaben da ba a taba samun irinsa ba a Najeriya, wajen yin komai a fili kuma cikin adalici.
Abiola dai ya rasu ne a gidan yari, a yayin da shugabannin duniya suke kokarin ganin gwamnatin soji ta Janar Sani Abacha ta sake shi.
Abin da ke ci wa ’yan Najeriya tuwo a kwarya
Wata malamar jami’a a Kaduna, Aisha Ismail, ta ce tun da Najeriya ta shiga Jamhuriya ta Hudu take fama da matsalolin tsaro iri-iri da ke barazana ga dorewar kasar.
Wani malamin makaranta a Kaduna, Reuben Silas, ya ce tilas ne gwamnati ta fara samar ta tsaro kafin tsarin dimokuradiyya ya samu bunkasa.
Mista Silas ya bayyana cewa bambancin tsarin dimokuradiyya da mulkin soji shi ne a dimokuradiyya jama’ar kasa ne ke da wuka da nama.
Tsugune ba ta kare kaba
A tsokacinsa game da cigaban da Najeriya ta samu a tsawon shekara 23 a karkashin mulkin dimokuradiyya, tsohon Editan Jaridar The Next a Jihar Neja, Mista Olu Jacobs, ya ce wannan abin farin ciki ne.
Sai dai ya ce duk da cewa kasar ta shafe sama da shekara 20 babu katsewa a bisa tafarkin dimokuradiyya, amma duk da haka babu wani sauyin ko zu ku gani da aka samu.
Hadiza Usman, wata mai yi wa kasa hidima ta ce babu wani kwakkwaran sauyi da ’yan Najeriya suka gani a cikin shekara 23 na mulkin dimokuradiyya a kasar.
“Babu canjin a zo a gani da dimokuradiyya ta kawo a Najeriya; hasali ma kamar ci baya muke samu, kuma rukunin shugabanni daya ne ke ta mulkar kasar,” a cewarta.
Shi kuma wani lauya, Hameed Ajibola Jimoh, ya bayyana cewa ’yancin ’yan Najeriya ne gwamnati ta kare musu rayuka, kuma kare rayukan nasu shi ne alamar kare tsarin dimokuradiyya.
Lauyan ya bayyana cewa duk inda aka samu tauye hakkin ’yan kasa, to tsarin dimokuradiyya na dab da zama tarihi a kasar.
Shin akwai dalilin yin bikin?
Wani kwararren mai ba da shawara kan harkar aikin jarida, Tony Abolo, ya ce bai ga abin da har za a yi biki ba.
Ya bayyana cewa irin dimokuradiyyar da ake gani a Najeriya ta sha bamban da irin wadda kasashen duniya take magana, ko ’yan Najeriya suke bukata.
Amma a nasa bangaren, wani malamin jami’a, Dada Ayokha, ya ce ya dace a yi murnar Ranar Dimokuradiyyar, tunda akalla ’yan Najeriya sun fita daga kangin mulkin soja.
Shi kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Mohammed Abdullahi, kira ya yi da a yi garambawul ga tsarin mulkin Najeriya da tsarin dimokuradiyyar kasar su dace da bukatu da kuma tsarin rayuwar ’yan kasar.
Malamai da jama’ar Kano
Masana a Jihar Kano sun yi bitar tafiyar dimokuradiyya a Najeriya a wani taro da suka gudanar a Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya ta Jami’ar Bayero (Gidan Mambayya).
A jawabinsa na maraba, Farfesa Isma’ila Mohammed Zango, ya jaddada muhimmancin masana da sauran masu ruwa da tsaki su yi kyakkyawan nazari kan yanayin tafiyar dimokuraiyyar Najeriya.
Shugaban taron, Sani Lawan Malumfashi, ya ce Najeriya na da aiki a gabanta, “Akwai bukatar magance tarin matsalolin da suka suka addabe mu, wadanda kuma mu ne kuma jawo su.”
Masanin Kimiyyar Siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fage, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su tabbata sun zabi shugabanni na gari.
Ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gbatar da makalarsa mai taken, “Tsarin doka da zabe a Najeriya: Bitar shekara 23 na tsarin dimokuradiyya a Najeriya” a wurin taron.
Mazauna Kano da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana damuwa cewa mulkin dimokuradiyya ya shekara 23 a Najeriya, amma har yanzu kasar ba ta gano bakin zaren abubuwan da za su ciyar da ita gaba ba.
Dole mu yi abin da ya dace a 2023 —Gwamnoni
A jawabansu na bikin zagayowar ranar, gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa ya zama wajibi jama’ar Najeriya ta yi abin da ya dace a zaben 2023 domin tabbatar da dorewar mulkin dimokuradiyya a kasar.
Gwamnonin sun yi kira ga ’yan kasar da su hada kai wajen wanzar da zaman lafiya da daidaito a fadin kasar.
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce dole ne shugabanni su nemo hanyoyin dakile matsalolin shugabanci, domin kawar da duk wata barazana ga tsarin dimokuradiyya.
Ya yaba wa ’yan Najeriya bisa hakurinsu da juriya wajen mara wa tsarin baya, gami da irin gudummawarsu wajen kawo cigaban kasa.
Don haka ya kara kira a gare su da su hada kai wajen ganin tabbatuwar dimokuradiyya, saboda duk da cewa tsarin na da matsalolinsa, amma shi ne tsarin shugabanci mafi aula.
Shi kuma Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, kira ya yi ga shugabanni da su jajirce wajen cimma burin shugabannin da suka kafa kasar ta hanyar samar da rayuwa mai nagarta ga al’ummomi masu zuwa.
Yahaya Bello ya ce kyakkyawan shugabanci shi ne kashin bayan samar wa al’umma da romon dimokuradiyya.
Daga Sagair Kano Saleh da Lami Sadiq (Kaduna), Abubakar Akote (Minna), Tijani Labaran (Lokoja), Haruna Gimba Yaya (Gombe), Christiana T. Alabi, Adelanwa Bamgboye (Lagos), Peter Moses (Abeokuta), Bola Ojuola (Akure), Bassey Willie (Yenagoa), Jude Aguguo Owuamanam (Owerri), Hassan Ibrahim (Maiduguri), Amina Abdullahi (Yola), Dickson S. Adama (Jos), Hope Abah Emmanuel (Makurdi), Ahmed Mohammed (Bauchi), Salim Umar Ibrahim & Zahraddeen Yakubu Shuaibu (Kano)