✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ci ka koshi…

A wani otel ne a Hadeja, aka rubuta a jikin allon sanarwa cewa: “Ka ci, ka sha iya yinka, amma jikanka ne zai biya kudin.…

A wani otel ne a Hadeja, aka rubuta a jikin allon sanarwa cewa: “Ka ci, ka sha iya yinka, amma jikanka ne zai biya kudin. Wani Bakatsine da ya ga haka, sai ya shiga otel din, domin dai ya san cewa ba shi ma da aure balle jika; wato zai ci banza ya tafi. Bayan ya ci abinci ya gama, sai ya ga daya daga cikin ma’aikatan otel din ya kawo masa takardar adadin kudin da zai biya. Bakatsine ya ce: “Ya haka? Ku fa kuka ce jikana ne zai biya kudin.” Ma’aikacin ya ce masa: “Ai da ma ba kudin da ka ci ne za ka biya ba, na kakanka ne da ya ci za ka biya, ga shi can a zaune.”
Daga Malam Babaji Hadeja, 07068068315