✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China za ta taimaka wa Najeriya wajen yakar ta’addanci

China za ta turo tawaga ta musamman da tallafawa jami'an tsaron Najeriya.

Kasar China ta ce za ta tura tawaga ta musamman ta kwararru kan binciken laifuka domin tattaunawa da hukumomin tsaron Najeriya, don taimakawa a yaki ta’addanci.

Jakadan kasar China a Najeriya Cui Jianchun ne, ya sanar da hakan a ranar Laraba a Abuja.

Ya ce China zata yi haka ne saboda ta damu kan matsalolin tsaron da Najeriyar ke fama da su.

Mista Cui ya kara da cewa wannan na daga cikin yunkurin gwamnatin China na kara karfafa alakar da ke tsakaninta da Najeriya.

Kazalika, ya ce kwararrun jami’ai na musamman daga China na dab da shigo wa Najeriya don tattauna yadda makamar aiki zai gudana tsakaninta da jami’an tsaron kasar nan.

Matsalar tsaro dai na daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya; wanda ya hada da Boko Haram, ISWAP, ’yan bindiga, IPOB da dai sauransu.