✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China ta ware $255m domin kammala aikin jirgin ƙasan Kano-Kaduna

Bankin Ƙasar China ya amince da bayar da Dala miliyan 254.76 domin kammala aikin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna.

Bankin Ƙasar China ya amince da bayar da Dala miliyan 254.76 domin kammala aikin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna.

Bankin ya amince ya ba da rancen ne gabanin ziyarar da Ministan Harkokin Wajen China, Mista Wang Yi, zai kawo Najeriya a wannan makon, inda ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba.

Aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna mai nisan kilomita 203 zai ci kuɗi Dala miliyan 973, kuma zai sada su da Abuja.

Aikin ya samu tsaiko amma Bankin na a China ya ba da tabbacin samar da isassun kuɗaɗe domin tabbatar da kammalawa cikin lokaci.

Ana sa ran sufurin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Abuja sai sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da harkokin kasuwanci tsakanin sauran sassan Najeriya da Kano, cibiyar kasuwanci.