✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China ta musanta zargin taimaka wa ayyukan ta’addanci a Najeriya

Wasu kamfanonin China na kulla yarjejeniya da ’yan fashin daji don samun biyan bukata.

Gwamnatin China ta musanta zargin cewa tana daukar nauyi tare da tallafa wa ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Bayanai na cewa ana zargin China na biyan ’yan ta-da-kayar-baya cin hanci don samun damar shiga wuraren ayyukan hakar ma’adanai a Najeriya.

A cewar China, ba za ta taba sa hannu a cikin duk wani abu da ya danganci tallafa wa ayyukan ta’addanci ba.

Martanin na zuwa ne bayan wani rahoto da Jaridar Times ta Birtaniya ta wallafa ranar 15 ga watan Afrilu, da ke cewa “Beijing na tallafa wa ayyukan ta’addanci a kaikaice” a Najeriya.

Wani bincike da kungiyar bin diddigin al’amura ta SBM da ke birnin Legas ta aika wa jaridar Times ya nuna wasu hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta irin na WhatsApp na wasu shugabannin ’yan ta-da-kayar-baya suna bugun kirjin cewa suna da karfin da dole duk wasu ma’aikatan China da ke son fara aikin hakar ma’adanai a yankunansu, sai sun biya su harajin kasa.

Sai dai wata sanarwa da Ofishin Jakadancin China a Najeriya ya fitar ta bayyana rahoton a matsayin “maras kan gado’’ inda ya kuma nuna rashin jin dadin gwamnatin kasar kan wannan rahoto.

“Zarge-zargen da ke kunshe a rahoton,” in ji sanarwar ofishin jakadancin China ba su da wani tushe balle makama, kuma akwai ayar tambaya game da rahoton.”

“Gwamnatin China da ma ofishin jakadancin China a Najeriya ko da yaushe suna karfafa gwiwa tare da yin kira ga kamfanonin China da ’yan kasar da ke zaune a Najeriya su kasance masu bin doka da oda.”

Jaridar HumanAngle ta intanet a Najeriya ita ma ta ba da rahoton cewa masu aikin hakar ma’adinai a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya suna biyan ’yan fashin daji harajin kashi 10% na abin da suke samu duk wata.

Manufar hakan ita ce su samu amincewa don ci gaba da ayyukansu na hakar ma’adinai.

Ofishin Jakadancin China a Najeriya dai ya jaddada cewa a tsawon shekaru da dama, dangantaka tsakanin China da Najeriya ta taimaka wajen bunkasa ci gaba mai amfani ga duk kasashen biyu da ma al’ummominsu.

“Don haka za mu ci gaba da aiki da gwamnatin Najeriya don tabbatar da ci gaban kasar da shawo kan matsalolin tsaro.

“Muna kuma maraba da abokan hulda na duniya, su shigo cikin wannan yunkuri amma za mu yi watsi da duk wata aniya ko matakin da zai gurbata alakarmu,” in ji sanarwar.

Jaridar Times dai ta kuma ruwaito cewa kamfanonin China a wuraren da ke fama da hare-hare na kulla yarjejeniyar tsaro da ’yan fashin daji da masu ta-da-kayar-baya.

Hare-hare kan ’yan China wadanda aka bayyana cewa yawansu a Najeriya ya kai tsakanin 100,000 zuwa 200,000, ya zama ruwan dare a shekarun baya-bayan nan a kasar wadda ke fama da matsalolin tsaro.

Tsakanin 2019 zuwa shekarar da ta gabata, rahotanni sun ce ’yan China 51 aka sace, tare da hallaka uku.

Akwai kuma yiwuwar cewa irin wadannan abubuwa da dama na faruwa su wuce ba tare da an ba da rahoto ba.