✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

China ta fuskanci zafi mafi tsanani tun 1961

A kwanakin baya bayan nan an fuskanci zafin da ya kai maki 35 a ma’aunin celsius ko ma fiye.

Cibiyar Kula da Yanayi ta kasar China (NCC), ta ce an fuskanci tsananin zafin da ba a taba fuskantar makamancinsa ba tun a shekarar 1961.

NCC ta ce daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga Agustan wannan shekara, an fuskanci tsananin zafi da ya kai maki 22.3 a maaunin celsius.

Cibiyar ta ce yankuna 17 daga kasar, ciki har da yankin Hunan da ke tsakiyar kasar, da Chongqin da ke Kudu maso Yamma sun fuskanci tsananin zafi.

Alkaluman da aka fitar a kwanakin baya bayan nan an fuskanci zafin da ya kai maki 35 a ma’aunin celsius ko ma fiye.

NCCn ta ce cibiyoyi 366 masu kula da yanayi a kasar sun ba da rahoton samun zafin da ya yi daidai da na wancan lokacin, ko ma ya haura.

Jimillar tashoshi 15 ne dai a kasar suka shigar da rahoton samun zafin da ya kai ko zarta maki 44 a ma’aunin celcius.

Cibiyar ta kuma yi hasashen cewa yanayin kaka a mafi yawan sassan kasar a bana, shi ma zai kasance fiye da yadda ya zo a shekarun baya.