Shugaban Kasar China, Xi Jinping, ya ba da umarnin gudanar sa kwarya-kwaryar bincike kan abin da ya haddasa hatsarin wani jirgin saman da ya yi sanadin salwantar rayukan mutum 132 a kasar.
Wani jirgin fasinja na kamfanin China Eastern dauke da fasinjoji 132 ya yi hatsari a ranar Litinin, bayan ya taso ne daga birin Kunming zuwa Guangzhou.
- Maryam Laushi: Damuwa da yadda za a dama da matasa
- Najeriya ce kasa ta 114 mafi samar wa ’yan kasa jin dadi a duniya —MDD
Hukumar Sufurin Jiragen Saman ta China ta ce jirgin, kirar Boeing 737 ya yi hatsarin ne a lokacin da yake dauke da fasinjoji 123 sai kuma ma’aikatan jirgin guda tara.
Lamarin dai ya ja hankalin al’umma, ciki har da Shugaba Xi Jinping, wanda ya bayyana kaduwarsa da kuma ba da umarnin gudanar da bincike nan take.
Hukumomin kamfanin China Eastern sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba su bayar da alkaluman mutanen da suka mutu ko kuma suka kubuta daga hatsarin ba.
Duk da haka, tuni dai kamfanin ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan fasinjojin da kuma ma’aikatansa da hatsarin ya rutsa da su.
Rabon da a samu hatsarin jirgin sama a China tun a shekarar 2010, inda hatsarin wani jirgi ya yi sanadiyar mutuwar mutum 42, daga cikin fasinjoji 92 da yake dauke da su.