Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadin cewa China na nuku–nuku tare da boye ainihin tasirin da annobar Coronavirus ta yi wa kasar – musamman ma alkaluman wadanda suka mutu.
Cire yawancin takunkumai da kasar ta yi a watan da ya gabata, ya janyo karuwar mutane masu kamuwa da cutar.
- Jama’ar Kano sun tabbatar da min da yakinin zan lashe zabe —Tinubu
- Sarkin dawa: Dabbar da ake jin gurnaninta daga nisan mil 5
Sai dai China ta daina wallafa alkaluman masu cutar a kowace rana, inda ta sanar da cewa mutum 22 ne kadai suka mutu sakamakon Coronavirus tun watan Disamba.
Darektan Bayar da Agajin Gaggawa na hukumar, Dr Michael Ryan, ya ce abin da suke gani a China kan cutar Coronavirus ba shi ne ainihin abin da yake faruwa ba musamman idan aka duba wadanda ake kwantar wa a asibiti da ke bukatar kulawar gaggawa da kuma wadanda ke mutuwa sanadin cutar.