✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China na fuskantar matsin lamba a MDD kan cin zarafin Musulmin Uighur

Kungiyoyin da ke yaki da take hakkin bil Adama na duniya, sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dau mataki kan kasar China…

Kungiyoyin da ke yaki da take hakkin bil Adama na duniya, sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dau mataki kan kasar China kan cin zarafin Musulmi ‘yan kabilar Uighur a kasarta.

koken na zuwa ne mako biyu bayan Hukumar kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta bankado wani rahoto da ke cewa kasar ta China na take hakkin Dan Adam a yankin Xinjiang.

A taron da majalisar da Kare hakkin bil Adama ta dauki nauyi, jami’i na musamman a majalisar, Fernand de Varennes, ya ce idan ba a dauki mataki kan Chinan ba, to al’umma za su yanke kauna da su.

Kazalika, mataimakin wakilin Amurka a majalisar ya ce daukar matakin na da alaka da yadda duniya za ta rika kallon Majalisar.

“Gaba daya sahihancin MDD ya ta’allaka kan matakin da muka amince za mu dauka kan kasar.

“Abin takaici ne a ce kasar da ta tallafa wajen ci gaban tsarin Majalisar Dinikin Duniya na zamani, kuma take cikin Kwamitin Tsaro ta majalisar, amma take take dokokinta,” inji shi.

Tun a shekarar 2018 ce dai kwamitin MDD da ke yaki da kabilanci a duniya ya bayyana cewa fiye da mutum miliyan daya ne ke tsare a wasu sansanoni da ke yankin Xianjiang na China.

Rahoton ya kuma bayyana yadda kafafen yada labarai suka gano yadda ake cin zarafin mutanen da ke sansanonin, hadi da tilasta su rabuwa da iyalinsu, da al’ada, har ma da addininsu.

To sai dai duk da hukumomin Chinan sun amince da akwai wadannan sansanonin, sun ce na horar da koyon sana’o’i ne ba abubuwan da rahoton ya bayyana ba.

Kasar ta kuma yi Allah-wadai da rahoton majalisar, da ta bayyana da karairayun kasashen yammacin duniya da ‘yan kanzaginsu.