✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta shiga zawarcin Osimhen da tayi mai gwabi

Chelsea ta shiga zawarcinsa duk da Manchester United da Tottenham sun nuna sha’awar daukar dan wasan.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana shirinta na ninka albashin da dan wasan gaba na Najeriya ke dauka a Napoli, Victor Osimhen.

Chelsea ta gabatar da tayin ne duk da cewar kungiyoyin Manchester United da Tottenham sun nuna sha’awar daukar dan wasan.

A cewar rahotanni, Chelsea na shirin dauko dan wasan da ya ke taimaka wa Napoli wajen ganin ta lashe gasar Serie A a karon farko a wannan karnin.

Kungiyar mai buga Gasar Firimiyar Ingila ta yi la’akari ganin yadda ya jefa kwallaye 19 daga cikin wasannin lik 21 da ya yi wa Napoli a kakar wasan bana.

A yanzu Osimhen ne mutum na biyu wajen daukar albashi mafi yawa a Napoli, inda ake biyansa shi Euro miliyan biyar kwatankwacin naira miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar a duk shekara.

Sai dai duk wannan tsabar kudi da dan wasan yake dauka, Chelsea ta ce a shirye ta ke ta ninka wa dan wasan albashinsa.

Chelsea na fuskantar kalubale daga bangaren United da kuma Tottenham wajen zawarcin dan wasan, inda Tottenham ke ganin dan wasan a matsayin wanda zai maye mata gurbin Harry Kane.