Kocin kulob din Chelsea da ke Sifen Jose Mourinho a shekaranjiya Laraba ya ce da kyar kulob din ya sha a hannun na PSG da ke Faransa a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai a ranar Talatar da ta wuce.
An tashi wasan ne da ci 1-1 amma yadda kulob din PSG ya rika kai munanan hari a bakin ragar Chelsea ta sa kulob din ya tsallake rijiya da baya inda aka tashi 1-1 a wasan ba tare da an samu nasara a kansa ba.
Mourinho ya ce ba karamar sa’a suka yi ba a wasan, ganin wasa ne da aka yi biji-biji da su amma a karshe aka tashi kunnen doki.
dan kwallon PGS Edison Cabani ne ya farke cin da dan kwallon Chelsea Ibanobic ya yi musu a wasan. Za a yi wasa karo na biyu ne a tsakanin kulob din biyu a ranar 11 ga watan Maris, 2015 a filin wasa na Chelsea don a samu wanda zai tsallake zuwa matakin kwata-fainal a gasar.