Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kulla damarar dawo da tsohon dan wasanta, Eden Hazard daga Real Madrid a matsayin dan wasan aro a karshen kakar wasanni.
Dan wasan ya sauya sheka daga Chelsea zuwa Real Madrid a 2019, amma rauni ya hana shi tabuka komai.
- Rahama Sadau ta sadaukar da kudin da ta tara a sabon fim dinta ga masu karamin karfi
- Babban Taron APC: Abin da ya sa Kwamitin Buni ke jan kafa
Lamarin da ya sanya shugabannin Real Madrid fara tunanin cefanar da dan wasan, tun da kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu.
Dan wasan mai shekara 30 ya samu tsaiko, inda Vinicius da Asensio suka sha gabansa wajen samun damar buga wasanni.
Tuni Chelsea ta tuntubi Real Madrid a ranar Litinin kan yiwuwar sake dawo da Hazard kungiyar a matsayin zaman aro, kuma tattaunawar ta yi nisa.
Ana sa ran idan dan wasan ya koma Chelsea, Kylian Mbappe zai maye rigarsa mai lamba 7 a kungiyar.