A daren yau na Asabar za a fafata tsakanin Chelsea da Manchester City a wasan karshe na gasar cin Kofin Zakarun Turai ta bana.
Kungiyoyin biyu wadanda suka fito daga Ingila za su kara ne a filin wasa na Estadio do Dragao da ke birnin Porto Kasar Portugal.
Wannan shi ne karon farko da City ta taba kai wa matakin karshe na gasar kuma take fatan lashe kofin a karon farko.
Ita kuwa Chelsea wanda wannan shi ne zuwanta na uku matakin karshe na gasar, tana fatan maimaita nasarar farko da taba yi a shekarar 2012 yayin da ta yi nasara a kan Bayern Munich.
Rahotanni sun bayyana cewa, annobar Coronavirus ta sanya ake tsammanin ’yan kallo 16,500 kacal ne za su shiga filin wasan domin ganin yadda za a kaya a wasan.
Wannan shi ne karo na hudu da kungiyoyin biyu za su kece raini a tsakaninsu a bana, inda bayan haduwa biyu da suka yi a gasar Firimiyar Ingila, sai kuma wacce suka yi a matakin daf da na karshe na gasar cin kofin kalubalen Ingila wato FA Cup.