Sarki Charles III ya karbi rantsuwar kama aiki a Asabar din nan a matsayin Sarkin Ingila bayan da Majalisar Nadin Sarki ta Birtaniya ta amince da cancantarsa.
Charles mai shekara 73, wanda shi ne Yarima Mai Jiran Gado, ya zama Sarkin Ingila ne kai-tsaye bayan Allah Ya yi wa mahafiyarsa, Sarauniya Elizabeth II cikawa a ranar Alhamis tana da shekara 96.
- Badakalar da Charles ya yi kafin zamansa Sarkin Ingila
- Mutuwar Sarauniya Elizabeth II: Me zai biyo baya?
Masu fada aji a Birtaniya ciki har da Firaminista Liz Truss da tsofaffin shugabannin gwamnatin kasar da ’yan Majalisun Dokoki sun halarci bikin nadin sarkin, wanda aka yi karkashi jagorancin Masu Nadin Sarki da ’yan gidan sarautar Ingila.
Tsofaffin Firaiministocin Birtaniya shida sun halarci nadin da suka hada da Sir John Major da Theresa May da David Cameron da Boris Johnson da Gordon Brown da Sir Tony Blair.
A cikin wani jawabi mai ratsa jiki, sabon sarkin na Birtaniya ya bayyana cewa yana sane da taya alhinin da duniya baki daya ta yi masu kan babban rashin da suka yi na mahaifiya.
Sarkin da ke kama ragamar mulki a wannan Asabar a hukumance, ya ce ya kwan da sanin irin nauyin da Sarauniya Elizabeth ta bar masa a matsayin gado.
Ya yi alkawarin aikata muhimman misalan da ya koya ta hanyar biyayya ga kundin tsarin mulki da tabbatar da ci gaba da zaman lafiya mai dorewa a Ingila da sauran kasashen duniya.
Bayan saka hannu kan sanarwar nada shi a Fadar St James ta birnin Landan, daga bisani an busa kakakin tabbatar da sarkin a wata cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Landan.
William ya zama Yarima mai jiran gado
Bayan nadin mahaifinsa a matsayin sarkin Ingila, Yarima William zai zama mai jiran gadon sarautar kasar lamarin da ke nuna nauyi zai karu a kansa wajen rungumar ayyukan masarauta sabanin a baya musamman bayan kaucewar dan uwansa Yarima Harry da kuma kawunsa Yarima Andrew.
William wanda ya girma da cikakken sanin iya kasancewa Sarkin Ingila a wani lokaci, shi ke dauke da nauyin ilahirin ayyukan Masarauta bayan ficewar dan uwansa Harry.
Masu sharhi na ganin William na da sa’ar iya dadewa a karagar mulkin Birtaniya, fiye da mahaifinsa wanda ke karbar sarauta y ana da shekaru 73 a Duniya bayan mutuwar mahaifiyarsa sarauniya Elizabeth ta 2 mai shekaru 96.
A zantawar Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP da Farfesa Robert Hazell, masanin ayyukan masarauta na Jami’ar College da ke birnin Landan, ya ce bayan nadin na yanzu, Yarima William mai shekaru 40 wanda tuni ya ke aiki da Sojin kasar zai karbi wasu karin ayyukan masarauta wanda a baya mahaifinsa ke tafiyarwa.
William da ke sahun fitattun iyalan sarautar Birtaniya da suka yi kaurin suna kuma suke da matukar farin jini ga al’ummar kasar, yanzu haka shi da matarsa Katherine za su zamo Yarima da Gimbiyar Cornwall sabanin Yarima da Gimbiyar Duke da su ke a baya.
Marubucin Masarauta, Phil Dampier ya ce tun daga haihuwar William a ranar 21 ga watan Yunin 1982 kaddara ta bayyana shi a matsayin wanda zai zama sarkin Ingila a gaba bayan gushewar mahaifinsa da yanzu ya karbi ragamar sarautar.