Liverpool za ta karbi bakuncin Villarreal a filin wasa na Anfield a daren ranar Laraba da misalin karfe 8 na dare.
Kungiyoyin za su kara a wasan kusa da na karshe na Gasar Zakarun Turai a zagayen farko.
- Ba don jajircewar Buhari ba da matsalar tsaro ta fi haka muni —Ayade
- ’Yan bindiga sun yi wa shugaban APC kisan gilla a Kaduna
Villarreal ta kasance kungiyar da ta bai wa kowa mamakin zuwa wannan mataki, bayan doke Juventus da Bayern Munich.
Kakar wasanni ta bana ta kasance wadda gwarazan na gasar Europa suka fi nuna hazaka.
Sai dai Liverpool za ta so gwada sa’arta a kan Villarreal don zuwa wasan karshe na gasar, wanda rabon da ta je wasan karshe na Gasar Zakarun Turai tun 2019.
Ana tunanin Villarreal za ta kara da Liverpool ba tare da ’yan wasanta irin su Gerard Moreno da kuma Alberto Moreno ba.
Ita kuwa mai masaukin baki, Liverpool, ana tunanin dan wasan gabanta, Roberto Firmino ba zai samu damar buga wasan ba, saboda rauni da yake fama da shi.
Ana hasashen Liverpool za ta fara wasan da ’yan wasa kamar su Alisson da Trent Alexander-Arnold da Ibrahima Konate da Virgil Van Dijk da kuma Andrew Robertson.
Sauran su ne Jordan Henderson da Fabinho da Thiago da Mohammed Salah da Sadio Mane da kuma Luis Diaz.
Ita kuwa Villarreal ana tunanin za ta fara ne da Geronimo Rulli da Juan Foyth da Raul Albiol da Pau Torres da Pervis Estupinan,
Sai kuma Dani Parejo da Francis Coquelin da Etienne Capoue da Giovani Lo Celso da Samuel Chukwueze da kuma Arnaut Danjuma.