Faransa da kawayenta da ke yaki da kungiyar masu da’awar jihadi a yankin Sahel sun goyi bayan yunkurin nada dan shugaban Chadi da aka kashe, Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya.
Shugaba Emmanuel Macron da takwarorinsa na kasashen yankin Sahel sun gana da Janar Mahamat Idriss Deby kafin jana’izar mahaifinsa, inji wani jami’in fadar shugaban kasar.
- ’Yar Sardauna, Aisha ta rasu
- Dan uwan Sarkin Musulmi ya rasu
- Yadda aka yi jana’izar Shugaban Chadi, Idriss Deby
Kasashen su ne Burkina Faso, Mali, Mauritania da Jamhuriyar Nijar.
Shugabannin sun nuna “hadin kan ra’ayoyi,” suna cewa “sun tsaya tare da Chadi tare da nuna goyon bayansu na bai daya ga tsarin mika mulki tsakanin farar hula da sojoji, don dorewar yankin”, inji majiyar.