✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya umarci bankuna su ci gaba da karbar tsoffin N500 da N1,000

Duk wanda ya kai tsoffin kudaden da suka haura N500,000 bakuna ba za su karba ba

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya umarci bankunan kasuwanci da su ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudin N500 da N1,000 daga hannun kwastomomi.

Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, sai dai ya ce duk wanda ya kai kudin da ya haura N500,000 kada bankunan su karba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin rai a fadin Najeriya kan haramta tsoffin takardun kudaden da gwamnati ta yi.

A cikin jawabin da ya yi wa ’yan Najeriya, Shugaba Buhari ya bukaci mutane da su kai tsofaffin takardun kudin N500 da N1000 ga CBN.

Hakan ya sa ’yan Najeriya yin dafifi zuwa ofishin CBN a jihohinsu don ajiye tsoffin takardun kudaden.

Yayin da jami’an bankin ke kokarin shawo kan jama’a, sun bukaci mutane da su kai kudadensu bankunan kasuwanci, amma mutane da dama sun ki yarda.

Tuni dai al’umma da dama a Najeriya suka bayyana jin dadinsu da Buhari ya kara wa’adin ci gaba da amfani da tsohuwar takardar N200.

Wasu kuma sun nuna damuwarsu kan yadda aka gaza samun isassun sabbin takardun Naira da CBN ta sauya.