Babban Bankin Najeriya (CBN) ya haramta wa bankunan kasar sallamar ma’aikata saboda matsin tattalin arzikin da annobar coronavirus ta haifar.
A wata sanarwa mai dauke da sa-hannun daraktansa na yada labarai, Isaac Okorafor, CBN ya ce an yanke shawarar hakan ne a wurin wani taro na musamman da bankin ya yi da Kwamitin Jagororin Harkar Banki ranar Asabar.
“Domin takaita mummunan tasirin da annobar COVID-19 za ta yi a kan iyalai da rayuwar mutane, babu wani banki da aka yarjewa ya sallami ma’aikata a ko wanne mataki ko ya dakatar da su”, inji sanarwar.
- COVID-19: Arik ya rage albashin ma’aikata da kashi 80
- Yadda kamfanin Gotel na Atiku ya sallami ma’aikata 54
Mista Okorafor ya kara da cewa an kuma cimma matsaya cewa kafin ko wanne banki ya sallami ma’aikata sai ya samu sahalewar CBN din.
Wannan mataki dai ya ceto ayyukan ma’aikatan bankin da ke fargabar yiwuwar rasa ayyukansu a yunkurin da bankuna ka iya yi na rage kashe kudi.
Tuni dai aka fara rage ma’aikata ko rage albashin da za a biya su a wasu bangarori na tattalin arziki, musamman harkar zirga-zirgar jiragen sama.
Kwanan baya kamfanin jiragen sama na Arik ya sanar da sallamar ma’aikata a irin wannan mataki na ririta abin da ya rage a lalita kasancewar wasu ba sa shigowa.