✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya fito da kai’idojin amfani da e-Naira

Ka'idojin za su shafi cibiyoyin hada-hadar kudade da daidaikun mutane.

Babba Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da wasu kai’idoji da sharuda da ya kamata a sani domin yin amfani da tsarin kudin intanet na e-Naira.

Aminiya ta gano cewa ka’idojin amfani da e-Naira za su shafi duk cibiyoyin hada-hadar kudade da kuma daidaikun mutane kamar yadda ya zo a cikin bayanin da CBN ya fitar.

Ka’idojin sun hada da: kafin fara amfani  da tsarin, dole za a bayyana yadda za a yi amfani da walet din e-Naira, ko amfanin mutum daya  ko a matsayin amintattu.

A karkashin Dokar CBN ta 2007 da Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kudi (BOFIA) ta 2020  ne kadai ke da alhakin lura da kuma raba kudin.

Darajar e-Naira za ta kasance daidai da ta Naira, za su rika tafiya kafada da kafada, kuma a karkashin kulawar CBN.

A cikin e-Naira walet ne kadai za a iya amfani da shi wannan kudin, sannan za a iya canza shi zuwa sauran kudaden duniya.