An yi bukukuwan cikar wata makabartar dabbobi irin ta ta farko a tarihi wacce ta ke a Kasar Italiya shekaru 100 da kafuwar ta a bana.
RFI ya ruwaito cewa, jama’ar kasar na ci gaba da tururuwa don kai ziyara ga dabbobin su da suka mutu daruruwan shekaru da suka gabata.
- ’Yan kwallo 20 da suka buga wasa fiye da 100 a Gasar Zakarun Turai
- ’Yan fashi sun kai hari Unguwar Maitama a Abuja
Wannan makabarta dai ta kasance makwancin karshe ga dabbobin jama’ar Italiya da kwanansu ya kare.
Jama’ar kasar dai sukan yi wa dabbobin jana’iza da kuma binne su cikin kaburbura tare da sanya shaidar mutuwa da alamomi tamkar dai yadda ake yi wa kaburburan ‘yan Adam.
Dabbobi irin su Maguna, Tattabaru, Karnuka, Jakuna, Dawaki, Zomo da sauran dabbobin gida, na daga cikin wadanda ke samu wannan gata daga jama’ar Italiya.
Dabbobin dai suna samun wannan karamci ta hanyar yi musu jana’iza da kuma binne su cikin wannan makabarta, yayin da iyalai ke kai musu ziyara lokaci zuwa lokaci don nuna alhinin rashin su.
Guda daga cikin dabbobin shahararrun mutanen da aka binne a makabartar sun hadar da kazar tsohon Shugaban Kasar Benito Mussoloni, kuma cikin shekaru 100 da makabartar mai suna Casa Rosa ta kwashe an binne dabobbi sama da 1,000.
Bisa al’adar al’ummar kasar dai a kan yi wa dabbobin ado tare da binne su cikin kaburburan da suka sha ado da duwatsu na alfarma da furanni masu kamshi.
Haka kuma, ana haka kaburburan dabbobin kasarkashin bishiyar dabino don kare su daga shan zafin rana.