. James Rodriguez dan kasar Kolombiya, dan shekara 23 ya koma kulob din Real Madrid da ke Sifen daga kulob din Monaco da ke kasar Faransa a kan Fam miliyan 71.
Rodriguez wanda ya fi kowane dan wasa zura kwallaye a Gasar Cin Kofin Duniya da aka gudanar a Brazil ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara 6 a Real Madrid.
Haka ya sanya ya zama dan kwallo na hudu mafi tsada a duniya bayan Gareth Bale da Ronaldo (dukkansu Real Madrid) da kuma Luis Suarez (Barcelona).
. Patrice Ebra ya canza sheka daga kulob din Manchester United zuwa Jubentus kan Fam miliyan 1.2.
Ebra ya koma Man United ne daga Monaco kan Fam miliyan 5.5 a shekarar 2006, inda ya buga wasa 379.
. dan kwallon Najeriya Brown Ideye mai shekara 25 da ke buga wasa Dynamo Kieb da ke kasar Ukraine ya koma kulob din West Bromwich Albion da ke Ingila a kan Fam miliyan 10.
. Kulob din Stoke City da ke Ingila ta cefano dan wasan gaba na kulob din Barcelona da ke Sifen, Bojan Krkic wanda kuma ke wasan aro a kulob din Ajad da ke kasar Holland kan farashin da ba a fada ba.
Canza sheka:
. James Rodriguez dan kasar Kolombiya, dan shekara 23 ya koma kulob din Real Madrid da ke Sifen daga kulob din Monaco da ke kasar…