✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin Rayuwa: Mun yi amfani da yajin aikin ASUU —Daliban jami’a

Saboda haka gaskiya ko an janye yajin aiki ba zan daina kasuwancin nan ba.

A Janairun bana, dalibi Isma’il Adamu ya samu gurbin karatu a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, wanda ya sa shi farin ciki, sannan ’yan uwa da abokan arziki suka shiga taya shi murna.

Nan da nan Isma’il mai shekara 18 ya harhada kayayyakin karatu da abinci da kayan sakawa ya bar Kaduna ya tafi Gusau domin fara karatu, da zimmar ya kusa cika burinsa na rayuwa.

Ashe dai kafin ya kammala murnar samun gurbin karatu, sauran murnar za ta koma ciki.

A tsarinsa, zai yi karatun digiri ya kammala yana da shekara 22 a duniya, wanda hakan zai ba shi isassshen lokaci ko dai ya kara karatu ko kuma ya fara aiki tun yana da sauran jini a jikinsa.

Sai dai kash! Kafin Isma’il ya isa jami’ar har an fara batun yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) za ta tsunduma.

Makonsa daya kacal a makaranta bayan ya fara karatu aka tafi yajin aikin gargadi. Daga gargadi kuma aka zarce na sai-baba-tagani.

Haka nan ya sake tattara wasu daga cikin kayansa ya dawo gida, ya bar abincinsa a can da tunanin zai koma bayan wasu ’yan kwanaki.

Idan ba a manta ba, Kungiyar ASUU ta fara yajin aiki ne a watan Fabrairu domin gargadi, sannan daga baya ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani da har yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana.

Daga yajin aikin gargadi, ana gobe za a koma, aka koma mako mai zuwa, aka koma batun wata – lamari ya yi kamari yanzu ana batun wata bakwai.

Kungiyar dai ta ce tana neman a inganta sakar wa jami’o’i kudaden gudanarwarsu ne sannan a biya su wasu hakkokin da suke bi da dai sauran bukatu.

“Gaskiya mun zaunu a gida, har mutum ya fara manta wasu abubuwan da aka koya masa a makaranta.”

Sai dai a daidai lokacin da dalibai ke jiran tsammani, domin a tunanin dalibai irinsu Isma’il na ba za a dade ba ana yajin aikin, shi kuwa iyayensa cewa suka yi ya je ya koyi sana’a.

“Wannan ya sa iyayena suka kai ni wajen koyon gyaran waya kuma Alhamdu lillah, yanzu ni dai ban yi zaman banza ba, duk da cewa na kosa a koma makaranta mu ci gaba da karatu.

Dalibin ya kara da cewa, “yanzu na koyi gyaran waya, ina samun na kashewa maimakon ina tsaye rokon kudi wajen iyayena.

“Duk da cewa iyayena ba sa gajiya wajen taimakona da sauran ’yan uwana wajen cika mana bukatunmu amma wannan dan zaman da na yi a gida ya taimaka min wajen koyon sana’a da a yanzu nakan biya wa kaina wasu bukatu.

“Ina matukar godiya ga iyayena da wannan tunani da suka yi, sannan ina godiya ga ogana wanda yake koyar da ni gyaran wayoyin da kasuwancin su da kuma rayuwa baki daya.

“Wannan dama ce da ba zan manta da ita ba saboda wasu irina yanzu haka suna gida ne suna zaman kashe wando.”

Burina na gaba:

Isma’il ya ce yanzu rayuwarsa ta riga ta canja domin a da can shi dalibi ne kawai da duk abin da yake bukata sai ya tambayi iyayensa amma yanzu ya san yadda zai iya juya taro ya koma sisi.

Ya ce, “ni yanzu ko na koma makaranta, zan ci gaba da aikina idan na samu hutu. In sha Allahu nan gaba ina da burin in bude katafaren shagon gyaran wayoyi da kayan aikin zamani da kuma sayar da wayoyi da kayansu.

“Dan zaman nan da na yi ya sa na fahimci abubuwa da yawa a rayuwa yanzu. Kuma tunanina yanzu ya canja a kan rayuwa.

Kira ga gwamnati:

Sai dai duk da cewa Isma’il ya koyi aiki kuma ba zaman banza yake yi a gidan ba, ya ce ya damu matuka da yanayin yadda yajin aikin yake tafiya.

“Gaskiya duk da na karu sosai da zaman, na kosa a koma makaranta mu ci gaba da karatu. Ina matukar kewar makaranta.

“Ilimi shi ne ginshikin komai a rayuwa. Don haka na fi son a koma makaranta mu samu mu karasa karatunmu.

“Wannan ya sa nake kira ga gwamnati da ta taimaka ta yi abin da ya dace domin a samu maslaha. Mu dai burinmu a samu matsaya, a daidaita mu koma makaranta.”

Shi ma Ibrahim Hafiz Umar matashi ne da ke aji daya a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ya ce kafin tafiya yajin aikin ASUU, yakan je kasuwa domin samun dan abin rufa wa kai asiri, sai dai tafiya yajin aiki ya tilasta shi maida hankali kacokan ga kasuwar.

“Sai na yi wata dabara na rika sayen kayan da ake yayi, irin su atamfa da leshi da kayan mata da dan abin da na samu a kasuwar.

“Da haka na fara saye da sayar da kananan kaya da riguna masu dogon wuya na zamani da ake ce wa “Turtleneck” har ma da jakunkunan mata da takalma a wasu lokutan. “Sai in dauke su a hoto da wayata in dora a shafukan sada zumunta.

“Kuma duk da ba ni da shago, daga gida nake sayarwa amma nakan samu akalla Naira 1,000 a kullum.

“Saboda haka gaskiya ko an janye yajin aiki ba zan daina kasuwancin nan ba, domin ina so in bunkasa shi ya zamo min silar rufin asiri in sha Allah,” inji Ibrahim.

Ita ma dai Fatima Nasir da ke zaune a Rijiyar Zaki, daliba ce da ke aji biyu a Jami’ar Bayero Kano. Kafin a fara yajin aikin, ta ce ta fara gwada sayar da yadukan zamani na mata ne kafin daga bisani ta hada da hijabai.

“Wani lokacin a mako daya sai in samu mutane biyu zuwa uku su saya, wani lokacin kuma babu amma dai idan an samu din akalla nakan samu ribar Naira 2,000.

“Gaskiya ko an janye yajin aiki ba zan bar sana’ata ba, domin ina son yi mata rajista ma a matsayin kamfani da sunan ‘The F Hijab Collections,” inji Fatima.

Khadija Ahmad Hanga mazauniyar Unguwar Yola ce da ke Kano kuma tana aji uku a Jami`ar Yusuf Maitama Sule.

Ta ce da fari ta fara ne da sayar da aya, da aka fara yajin aiki sai ya zama sayen katin waya don zagaye a yanar gizo na gagarar ta, “sai wani dan uwana da ya zo ya ci wani taba-ka-lashe da ake ce wa ‘Doughnut’ da na yi, ya ce me zai hana in fara sayarwa?

“Haka kuwa aka yi amma da farko gaskiya ba a saye sosai, sai dai idan ya yi kwantai na raba wa kawayena.

“Lokacin da sana’ar ta yi karfi, shi ne lokacin da na fara Ministan Ilimi Adamu Adamu hadawa da wani taba-ka-lashen zamani da ake sarrafawa da garin filawa mai suna Brownie, da shi kadai nakan samu Naira dubu 18 a rana daya.

“Kuma fa ba shi kadai nake sayawar ba, akwai wasu abubuwan da dama na makulashen.

“Gaskiya ba zan daina sana’ata ba, domin duk da ba ni da shago daga gida nake ciniki, har na yi rajistar kamfani da sunan Snacks Delicia.”

Halin da ake ciki kan yajin aikin:

A farkon makon jiya ne aka wayi gari da batun umarnin Gwamnatin Tarayya ga shugabannin jami’o’in Najeriya da su koma bakin aiki.

Wannan umarnin ya biyo bayan hukuncin kotu ne, inda kotun ta bukaci malaman jami’o’in su koma bakin aikinsu, wanda ita ma kungiyar tuni ta daukaka kara.

Sai dai kuma kimanin sa’o’i 24 da sanarwar ce aka samu wata sanarwar cewa Gwamnatin Tarayya ta janye umarnin.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin NUC, Haruna Lawal Ajoh, ya ce an janye umarnin ne saboda wanda ya rattaba mata hannu mukaddashi ne a kan kujerar.

Kazalika, Haruna ya kuma ce Ministan Ilimi da Shugaban Hukumar NUC sun tattauna sannan sun amince da janye umarnin.