✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin kudi zai fi tagayyara ’yan siyasa a kan talakawa —Sanusi

Sarkin Kano na 14 ya ce tsarin zai taimaki talakawa wajen zabar wanda suke so.

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi  II, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan canjin kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

Wannan na dauke ne cikin wani sakon bidiyo da Sanusi ya wallafa a kafofin sada zumunta, inda ya bukaci kada talakawa su yarda su fada tarkon ’yan siyasa.

Ya bayyana cewa canjin kudin ba sabon tsari ba ne, ya kai shekara 10 da fitowa.

Da yake sukar ’yan siyasa, Sanusi ya ce sauyin kudin ya tagayyara su tare da lalata burinsu na satar dukiyar kasa.

“Wannan tsari ne da ya fi shekara 19 da fitowa.

“Shawarata ta biyu ga ’yan Najeriya, shi ne kada su yarda da abin da ’yan siyasa ke fada.

“’Yan siyasa sai sun fi daidaikun mutane shiga wahala game da wannan tsari.

“Sun shafe shekara hudu suna satar kudi suna azabtar da mutane, yanzu saboda zabe ya zo sun fito da kudi suna sayen kuri’u da jami’an INEC da daukar nauyin ’yan bangar siyasa.

“Tsarin zai rage magudin zabe, idan kana son bai wa jami’in INEC, dan sanda ko wani kudi, ka tura masa ta banki ta yadda za a iya bin diddiginsu.

“Ya kamata ’yan Najeriya su karbi wannan tsari hannu bibbiyu saboda zai ba su damar zabar wanda suke so, ba wadanda za su dauki hayar ’yan dabar da za su murde musu zabe ba.

“A baya wadanda suka fi kowa satar kudi su suka fi yin magudin zabe.

“Yanzu kuwa ko mutum ya boye kudi ba su da amfani saboda an sauya su,” in ji shi.