Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin jam’iyyar APC.
Tattaunawar da aka yi a Fadar Shugaban Kasa a Abuja ta samu halartar shugaban gwamnonin, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.
- Babu kasar da ta taba sauya kudi a lokacin zabe sai Najeriya —El-Rufai
- Mutum 10,000 sun kamu da ciwon daji cikin wata guda a Najeriya
Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna; Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano; Dave Umahi na Ebonyi; Babajide Sanwo-Olu daga Legas; Dapo Abiodun na Jihar Ogun da Simon Lalong na Jihar Filato.
Ganawar na zuwa ne bayan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa akwai wasu kusoshi a fadar shugaban kasa da ke kokarin kawo cikas ga nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Sai dai Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya ce a hukumance gwamnati ba ta da masaniyar wani a fadar shugaban kasa da ke yi wa Tinubu zagon kasa.
Ya ce gwamnatin Buhari ta yi wa kowa adalci ba tare da la’akari da jam’iyya da ya fito ba kuma shugaba Buhari ya lashi takobin gudanar da sahihin zabe.
El-Rufai ya yi wadancan kalamai ne a wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce kusoshin na son ganin Tinubu ya fadi sakamakon gaza lashe zaben fid-da-gwani da dan takararsu ya yi.
Sai dai kalaman nasa sun tada kura, kuma ana kyautata zaton ganawar da Buhari ya yi da gwamnonin na APC na da nasaba da kalaman na gwamnan Kaduna.