✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canja dokar gado: Duk Musulmin da ya taimaka ya yi ridda – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya gargadi ’yan Majalisar Dattawa dangane da wata doka da suke tattaunawa a kanta da take…

Fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya gargadi ’yan Majalisar Dattawa dangane da wata doka da suke tattaunawa a kanta da take neman daidaita maza da mata wajen rabon gado, inda ya ce duk Musulmin da ya taimaka aka canja dokar gado yana  iya fita daga Musulunci wato ridda.
Shehin Malamin ya gargadin sanatocin ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a gidansa da ke Bauchi a shekaranjiya Laraba, inda ya ce dokar da sanatocin ke neman kafawa, ta saba wa addinin Musulunci, ta bangaren rabon gado tsakanin maza da mata, domin kuwa maza na da kaso biyu ne a kan mata, kamar yadda Allah Ya raba da kanSa. Ya ja hankalin sanatocin da duk masu rike da madafun iko su rika taka-tsantsan da duk wasu al’amura da suka shafi addinan al’ummar Najeriya.Sheikh dahiru Bauchi ya gargadi sanatoci Musulmi cewa kada su kuskura su sanya hannu kan dokar. Ya ce su sani cewa, muddin suka goyi bayan dokar, sun  bi son rayukansu ne  kawai, domin canja dokar gado ta saba wa Allah, saboda Allah Ya bayyana tsarin rabon gado dalla-dalla a Alkur’ani Mai girma.