✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

CAN ta musanta goyon bayan takarar Tinubu

Kowa ya sani ba ma goyon bayan takarar musulmi biyu a tikiti daya.

Kungiyar mabiya addinin Kirista ta Najeriya (CAN) ta ce batun da wasu kaffofin yada labarai ke yadawa kan ta koma goyon bayan takarar Tinubu shaci-fadi ne kawai.

Cikin wata sanarwa da Kakakin kungiyar Luminous Jannmike ya fitar dauke da sa hannun shugabanta Daniel Okoh, ya ce babu kamshin gaskiya a rahoton, don haka al`umma su yi watsi da shi.

“Al`umma su sani ba ma goyon bayan takarar musulmi da musulmi a Najeriya, kuma tun daga shugaban kungiya har sauran kiristoci na kasa duk matsayarmu kenan.

“Sai dai muna sane da cewa jam`iyun siyasa na da damar daukar matsayar da ta yi musu muddin ba ta saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da Dokar Zabe ta 2022 ba”, a cewar sanarwar.

CAN ta kuma ce a matsayinta na kungiya mai zaman kanta, za ta ci gaba da hada guiwa da dukkan shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki don samar da hadin kai, da zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Shugaban ya kuma bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu da su sanya Najeriya a gaba a dukkanin al’amuransu, su kuma shirya yi wa jama’a hidima da gaskiya da rikon amana.