✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CAF ta ci tarar Najeriya saboda cunkoso a filin wasa na Ahmadu Bello

Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (CAF) a ranar Litinin da ta gabata ne ta bayar da sanarwar cin tarar Najeriya Dala dubu 5 saboda…

Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (CAF) a ranar Litinin da ta gabata ne ta bayar da sanarwar cin tarar Najeriya Dala dubu 5 saboda cunkoso a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.
A wasan da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta yi da ta Masar a ranar 25 ga watan Maris da ya gabata ne kimanin magoya baya dubu 40 suka shiga filin wasa na Ahmadu Bello don kallon yadda wasan ya kaya.  Sai dai a ka’ida filin bai wuce ya dauki ’yan kallo dubu 16 ba amma sai ga shi ya dauki kusan dubu 40.  Hukumar CAF ta ce yin haka ya saba wa ka’ida don haka ne ta ci tarar Najeriya.
Cunkoson ya samo asali ne bayan  gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i ta sake tikitin shiga wasan inda ta umarci a bar magoya baya su shiga filin wasan kyauta ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba.  Hakan ta sa aka samu cunkoso, maimakon a samu magoya baya kimanin dubu 16 sai aka samu kusan dubu 40.  Sai dai duk da haka an yi wasa kuma an kare lafiya ba tare da an samu wani hargitsi.
Masana harkar kwallo sun ce Najeriya ta auna arziki ganin yadda aka yi wasa lafiya kuma aka tashi lafiya ba tare da an samu wani yamutsi ba.
Kan haka ne hukumar CAF ta yi nazari inda ta ci tarar Najeriya Dala dubu 5 kwatankwacin Naira Miliyan 1 da dubu 610 don ya zama darasi.
Sannan Hukumar CAF ta ci tarar Masar Dala dubu 5 a wasa zagaye na biyu da ya gudana a Masar inda Masar ta samu nasara a kan Najeriya da ci 1-0.  Jim kadan bayan an tashi wasan ne magoya bayan Masar suka nuna rashin da’a ga ’yan kwallon Najeriya.
Idan za a tuna Masar ta fitar da Najeriya daga halartar gasar cin kofin Afirka da zai gudana a shekara mai zuwa ne bayan ta samu nasara a kan Najeriya da ci 2-1 idan aka hada wasannin biyu.