Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta umarci jami’in sojin Faransa da ke aiki a ofishin jakadancinta na kasar Emmanuel Pasquier ya tattara kayansa ya fita daga kasar nan da mako biyu.
Lamarin dai na zuwa ne bayan an zargi Pasquier da shirya wa kasar makarkashiya, kamar yadda wasu bayanai da Kamfanin Dillancin Labaran AFP ya ce ya samu daga muhukumta suka nunar.
- Mai A-Daidaita-Sahu ya mayar da N15m da fasinja ya manta a babur dinsa
- Wanda ya kashe jaririyarsa mai kwana 1 ya shiga hannu a Kano
“An kori jami’in tsaron tare da sauran jami’an tsaro da ke ofishin sojin Faransa da ke babban birnin kasar Ouagadougou,” kamar yadda gidan rediyon Omega ya ambato wata sanarwa da hukumomin kasar suka aike wa ofishin jakadancin Faransa da ke kasar.
A cikin wata wasika da ma’aikatar harakokin wajen Burkina Faso ta aika wa mahukumtan birnin Paris a ranar alhamis 14 ga watan satumba 2023, Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da soke izinin zaman kasar, da ta bai wa M. Emmanuel Pasquier, babban jami’in da ke kula da huldar soji a ofishin jakadancin Faransa da ke Ouagadougou, babban birnin kasar, saboda wasu dalilai da ta ce, na zagon kasa ne da jami’in ke yi ga kasar, inda ta bashi wa’adin makwanni biyu, da shi da tawagarsa su tattara nasu ya nasu su fice mata daga kasa.
Kazalika wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Burkina Faso ta fitar ta shaida wa Faransa cewa Burkina za ta yi gaggawar rufe ofishin sojojinta da ke Paris, a cewar rahoton.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da Burkina Faso bayan juyin mulkin watan Satumba na 2022 wanda ya dora Kaftin Ibrahim Traore a kan mulki.
A watan Janairu Burkina Faso ta daina huldar soji da Faransa, sannan ta bai wa tsohuwar uwar gijiyarta wata daya ta janye dakarunta daga kasar inda ta dade tana yaki da kungiyoyin ta’addanci irin su al-Qaeda da Daesh/ISIS.