Gwamnatin mulkin soja ta Burkina Faso ta bukaci dakarun kasar Faransa da su bar kasarta nan da wata daya.
Matakin, wanda Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar (AIB) ta sanar da dauka ranar Asabar na nuna yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin Burkina Faso da kasar da ta taba yi mata mulkin mallaka.
- Kona Alkur’ani a Sweden ya jawo Allah-wadai daga kasashen Musulmai
- 2023: Babu dan Najeriyar da ya san ciwon kansa da zai zabi APC – Gwamnan Bayelsa
Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta fara yin tsami ne tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Satumbar bara.
AIB ta ce a ranar Laraba gwamnatin ta dauki matakin yi fatali da yarjejeniyar sojoji ta 2018 da ta ba dakarun na Faransa damar yin sansani a cikin kasarsu.
Sai dai har yanzu gwamnatin Faransar ba ta ce uffan ba a kana matakin.
Wata majiya daga gwamnatin sojan ta Burkina Faso ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) a Ouagadougou babban birnin kasar cewa babu wata matsala tsakanin kasashen biyu, sai dai kawai gwamnatin na nuna damuwa ne kan ci gaba da zaman sojojin Faransar a kasar.
Faransa dai na da dakaru kusan 400 a Burkina Faso, kasar da take ta fama hare-haren ’yan ta’adda masi alaka da kungiyoyin ISIS da Al-Qaeda.
A ’yan watannin nan dai, yawan kin jinin Faransa ya karu a kasar matuka, yayin da mutanen kasar da dama ke da ra’ayin cewa ci gaba da zaman dakarun ne ummul-aba’isun matsalolin tsaron kasar