✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina shi ne Tinubu ya tilasta wa maza kara aure —Rashida Mai Sa’a

Tsohuwar Hadima ta Musamman ga Gwamnan Kano kuma fitacciyar jarumar Kannywood, Rashida Mai Sa’a ta ce babban fatanta shi ne gwamnatin Bola Tinubu ta tilasta…

Tsohuwar Hadima ta Musamman ga Gwamnan Kano kuma fitacciyar jarumar Kannywood, Rashida Mai Sa’a ta ce babban fatanta shi ne gwamnatin Bola Tinubu ta tilasta wa magidanta su kara aure.

A hirarta da manema labarai, Rashida ta kara da cewa baya ga haka, tana fata gwanatin za ta dauke musu nauyin kayan aure.

“To mu dai babu abin da muke so Baba Tinubu ya yi mana kamar dauke mana wahalhalun aure da kuma sanya wa duk mai mace daya ya kara, mai biyu ma haka, mai uku kuma ya cike.

“Sannan kuma muna so a ba mu sana’a, wadanda suke da shaidar karatu kuma a ba su aiki.

“Ita ma kuma matar shugaban kasa muna so ta yi koyi da abin da Aisha Buhari ke mana, yadda ta ke debo mu ta saka mu a gaba-gaba”.