✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina shi ne taimaka wa mata da yara da kuma nakasassu – Hajiya A’isha Atiku Bagudu

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta kafa wata kungiya domin taimaka wa mata da yara da nakasassu da marayu. Ta…

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta kafa wata kungiya domin taimaka wa mata da yara da nakasassu da marayu. Ta bayyana haka ne a  hirarsu da wakilinmu.  Ga yadda hirar ta kasance kamar haka:

Aminiya: Hajiya mene ne dalilin kirkiro wannan kungiya kuma yaya sunanta?
Hajiya A’isha: Bismillahi rahamanir Rahim.   Da farko dai ita wannan kungiya mun sanya mata suna (MALLPAI) kuma abin da ya sa muka kirkiro wannan kungiya shi ne saboda mu taimakawa mata da yara da nakasassu da marassa galihu. Kuma za ka ga a duk lokacin da talakawa suka yi zaben sababbin shugabannin da za su wakilce su a mukaman gwamnatocin jihohi da na tarraya, to, za su koma gefe ne kawai suna sauraron irin abubuwan alherin da za su inganta rayuwarsu ta kowace fuska ganin cewa, wannan shi ne hanyar da talakawa za su ci moriyar dimokuradiyya. Akan haka ne muke son mu bunkasa harkokin rayuwar mata da kananan yara da marayu da kuma nakasassu duk da cewa wannan kungiya ba ta gwamnati ce ba,  kuma ba ta da alaka da gwamnati.
Aminya:  Wane irin taimako kungiyarku take yi?
Hajiya A’isha: kungiyarmu tana taimaka wa marayu wajen ba su abinci da kuma sai masu kayan sawa, haka kuma muna tura yara zuwa makarantu da dinka masu kayan  makaranta. Akwai shiri na musamman da za mu fito da shi domin  koyon  sana’o’i ga mata da yara domin dogaro  da kai.   Haka su ma  nakasassu kungiyarmu tana taimaka masu ta kowane bangaren rayuwarsu, idan bukatar hakan ta taso. Muna son kafin nan da shekara 2017 a kowace hedikwatar karamar hukumar Jihar Kebbi mu bude cibiyar koyon sanao’i na mata da yara, haka su ma matan aure ba za mu bar su  a baya ba.
Aminiya:  Baya ga taimakon da kungiyarku ke yi ga yara da marayu, ko akwai wani shiri game da taimakawa mata masu ciki?
Hajiya A’isha:  Na ji dadi da wannan tambaya, ai mata masu ciki kusan in ce su ne  a sahun gaba wajen bada taimako, domin  su ke bukatar taimakon a cikin gaggawa, saboda duk taimakon da muke bada wa ga yara idan iyaye mata b asu haihu ba aka samu yaran ina za mu bada taimako? Saboda haka yanzu mun fara sayen magunguna domin rarrabawa ga kanannan asibitocinmu na karkara domin baiwa mata masu ciki da kuma naksassu da yara kanana, kuma yanzu haka a nan gaba kungiyarmu za ta fito da shirin adana jini domin agazawa da kuma rage yawan mace-macen mata masu ciki da kananan yara saboda rashin isassashen jini. Saboda mun lura cewa, rashin wadataccen  jini ga mace a lokacin haihuwa ke kawo rashin uwa ko da a lokacin haihuwa musamman a karkara inda babu asibitoci.
Aminiya:  Ko akwai wani tallafi da za ku yi wa samari  musamman ta fuskan ilimi?
Hajiya A’isha:- Samari matasa ai su ne abin taimaka wa wajen karo ilimi, domin su ne manyan gobe.   kungiyarmu tana da kyakkyawar niyya ta fuskar daukar yaran da aka kora a makaranta da yaran  da suka gudu daga makaranta da wadanda iyayensu suka kasa taimaka masu dalilin rashin kudi.   Wannan zai taimaka wa yara wajen kawar da hankalinsu daga aikata aikin assha da zaman kashe wando da shaye-shaye a cikin al’umma.
Aminiya:   A  matsayinki na uwa, me za ki ce game da illar talla ga ’ya mace?
Hajiya A’isha:  Na san wani lokaci wasu iyayen ba a son ransu suke sa ‘ya’yansu talla ba, hakan na faruwa ne saboda wasu dalilai da suka sha karfinsu. Misali, za ka ga mace na rike da  marayu, ba ta mallaki komai ba, haka nan babu mai tallafa mata ita da ‘ya’yanta sai Allah.  Wannan dalilin  yakan zamo wa wasu matan dole su tura’ya’yansu  talla su rika juya dan jarin da suke da shi domin su samu na abinci.
Wani lokaci kuma zai iya kasancewa mahaifin yaran na raye amma ba shi da lafiya, ko yana tare da wata lalurar da ba zai iya fita neman abinci ba, Ta hakan matar kan tura ‘ya’yansu talla domin tallafa wa gidan.  Idan muka juya ta wani fannin kuma sai mu ga mutuwar zuciya da yawan son abin duniya su ke  sa wasu iyayen suke tura ’ya’yansu talla. Na kuma fi dora wannan laifi ga iyaye mata.
Za ka ga wani magidanci yana iyakacin kokarinsa wajen biyan bukatun iyalinsa, ya kuma sa ‘ya’yansa a makaranta, amma uwarsu baz a ta bar su su yi karatu ba, sai ta rika tura su talla saboda wani dalili nata na son kece-raini cikin tsara,  kamar yadda wasu matan kan ce.  Akwai macen da ita kanta ta san ba ta mallaki komai ba, hasali ma dan jarinta bai taka kara ya karya ba, amma sai ka ga tana bada makudan kudi a wajen biki, da sunan gudunmawa, wai don ita ma in ta tashi nata bikin a tara mata abin duniya. Hakan ke sa wasu matan tura ’ya’yansu talla domin tara kudin zuwa biki.
Wata kuma ta kan ce ai wance  ta cika wa ‘yarta daki da kayan alatu, saboda haka ni ma ba zan aurar da ‘yata ba sai na tara abin da mutane za su yaba, Da irin wannan tunanin sai ka ga an tura ’ya’ya talla wai  don a rika yin tari.
Na farko dai babar illa da ke tattare da ’yan talla wato rashin tarbiyya.  Daga yadda ‘yar talla ke tafiya, zuwa lafuzzan da ke fita daga bakin ta da kuma yadda take mu’amala  da masu yi mata ciniki musamman ma maza za ka fahimci cewa, wannan yarinya ba ta da tarbiyya. Ba  zan yi mamakin hakan ba saboda mahaifiyar yarinyar nan babu wata kwakkwarar tarbiyyar da ta ba ta. Sai dai kowa mata yadda za ta yi kwalliya da wuraren da za ta bi domin ta samu ciniki.
Idan kuma yarinyar nan ta fita gida tun safe, wata ba ta komawa sai da yamma ko dare. Ka ga ina maganar koyar da tarbiyya a nan? Uwar ma ba ta san inda yarinyar ta yini ba, balle kuma ta damu da ta yi salla ko ba ta yi ba.
Illa ta biyu ita ce, rashin  ba yara masu talla damar zuwa makaranta.  Na san da cewa, wasu yaran sukan je makaranta su kuma yi talla, amma wasu za ka ga gaba daya ba su zuwa makaranta, babu ilimin addini ballantana kuma na zamani.   Akwai illoli da dama  da talla ke haifarwa, idan na ce zan zayyano su duka sai mu kai wani lokaci ban gama ba.
Aminiya:  Bayan  tallafi da kungiyarku ke yi ko akwai wani abu da ke ci maku tuwo a kwarya?
Hajiya A’isha:   Na ji dadin wannan tambaya. Abin da ke ci mana tuwo a kwarya babu kamar yadda ake yi wa yara mata kanana fyade.   In Allah Ya yarda duk lokacin da kungiyar mu ta samu wanda ya yi fyade za mu tsaya tsayin daka mu ga an hukunta shi ko shi wanene. Haka ku ma ‘yan jarida akwai gaggarumar rawar da za ku taka akan wannan al’amarin, saboda haka kungiyarmu tana neman hadin kanku,kuma kun zama membobi domin bada taku gudummuwa. Domin kun san ita wannan  kungiyar ba ta da wani alaka da gwamnati, amma kuma idan gwamnati za ta bada taimako a ashirye take ta karba, kuma tana goyon bayan gwamnati akan taimakawa yara kanana da mata masu ciki da kuma yara marasa galihu da nakassassu.
Aminiya: Nagode da kika ba ni dama har muka tattauna da ke.
Hajiya A’isha:  Ni ma na gode da ka kula da kungiyarmu.  Allah Ya taimaka ka da sauran ma’aikatanku baki daya, na gode.