Hajiya Ummi Tanko Yakasai ita ce Shugabar Jam’iyyar Matan Arewa reshen Jihar Kano. A tatatunawarta da Aminiya ta bayyana cewa babban burinta a rayuwa shi ne ta ga matan Arewa sun tsaya da kafafunsu ta hanyar neman na kansu. Da sauran batutuwa da suka shafi mata.
Tarihina:
Sunana Ummi Tanko Yakasai. An haife ni a 1961 a Unguwar Sabuwar Yakasai. An fara sanya ni a makarantar allo ta Malam Dan Sakkwato. Sannan a 1968 aka sanya ni a firamaren Shahuci a rabin aji. Ina aji sai aka ba mahaifina mukamin Kwamishina don haka muka tashi daga cikin gari muka koma Unguwar Nasarawa. Hakan ya janyo aka yi mini canjin makaranta inda na koma firamren Magwan. Sai dai ban kammala a makarantar ba domin an kai ni makarantar kwana ta sakandare da ke Shekara. Bayan na kammala sai na tafi sakandaren Saint Louse. Ina makarantar ce sai mahaifina da sauran jama’ar Jihar Kano suka bude Makarantar Al’umma ta Kano Kwamashiya. Sai dai kuma mutanenmu ba su karbi makrantar ba, sai ya zama sauran kabilun da ke jihar ne kawai ke amfana da makarantar.
Hakan ya janyo wadanda suka bude makaranar suka yi tunanin kawo ’ya’yansu makarantar don zama abin misali ga sauran al’ummar Jihar Kano. sai aka dauko ni da dan uwana Ibrahim Allah Ya jikansa aka sa mu a makarantar.
Lokacin muna dalibai a makarantar kwararru a fannoni daban-dabn sukan ziyarce mu don wayar mana da kai a kan aikinsu. Da farko ina sha’awar aikin lauya, amma wata rana da masu aikin taimakon al’umma suka zo sai suka canja mini tunani na ji ina sha’awar aikinsu don haka da na tashi neman gurbin karatu sai na nemi Makarantar Kimiyya da Kere-Kere ta Kano inda na karanci bangaren harkokin rayuwa (Social Administration). Ina cikin wannan karatu na yi aure na kuma fara haihuwa.
Ayyukana:
Bayan na kammala karatu sai na fara aiki da gwamnatin Jihar Kano a 1983 a Ma’aikatar Inganta Rayuwar Jama’a lokacin ma’aikata ce mai zaman kanta inda aka tura ni gidan marayu na Nasarawa a matsayin mai kula da yaran da ke gidan. Irin wadannan yara sun hada da wadanda ake zubar da su a kwararo ko a kasuwanni. Akwai wadanda suka bata aka rasa iyayensu. Akwai ’ya’yan mahaukata, akwai ’ya’yan takari da ake kamo su daga Saudiyya. Irin wadannan ’ya’yan su ne wadanda ake bayar da su ga wadanda suke son su rike ’ya’ya, saboda babu ainihin iyayensu, don haka idan aka bi ka’idoji mukan bayar da su saboda mu kanmu ba mu son ’ya’yan su girma a haka har su san matsayinsu.
Na kuma yi aiki a gidan masu tabin hankali na Dawanau inda muke kula da masu tabin hankali sanadiyyar shaye-shaye ko damuwa. Muna ba su shawarwari da jan hankalinsu.
Haka kuma na yi aiki a makarantar koyon sana’o’i ta nakasassu ta musamman inda suke koyon saka da aikin kafinta da sauransu. Idan suka koya mukan sama musu kasuwa su sayar da kayayyakin nasu. Haka kuma idan sun kware mukan kai su kamfanoni don a dauke su aiki domin su zama masu dogaro da kansu.
A 1985 sai Kwamishina A’isha Isma’il ta fito da wani tsari na sama wa mata ma’aikata wurin da za su rika ajiye ’ya’yansu a lokacin da suka tafi aiki inda ta bude wurin a Unguwar Gyadi-Gyadi aka kuma dauki ma’ikata masu kula da yaran , inda mu kuma aka kai mu a matsayin masu kula da wurin gaba daya. Babu shakka a wanann lokaci mata ma’aikata sun samu natsuwa, domin sukan je aiki ko makaranta ba tare da damuwa ba kuma a farashi mai rahusa.
Ana nan sai maigidana ya samu canjin aiki zuwa Abuja. Lokacin Abuja ba ta kafu sosai ba, don mu ne muka bude ofishin kula da jin dadin jama’a (Social Welfare) inda na nuna yi musu yadda ake harkar gidan marayu, domin gidan marayu na farko da aka fara kafawa a Abuja a Karu mu ne muka kafa shi.
A 1992 sai muka koma Kano inda Kwamishina ta ba ni zabin bangaren da nake son yin aiki. Ni kuma sai na zabi bangaren matasa inda muka rika yi wa kungiyoyi rajista. Sannan muna halartar tarurrukan kungiyoyin don tabbatar da cewa abin da suka fadi suna aiwatar da shi. Wannan aiki ya sa na shiga lungu da sako na Kano har ma kuma na saba da jama’a.
Aikina a Jam’iyyar matan Arewa:
Jam’iyyar Matan Arewa kungiya ce mai zaman kanta wacce Sa Ahmadu Bello Sardauna ya kafa a 1963 da nufin sama wa matan Arewa wani dandali da za su rika magana da murya daya da nema wa kansu mafita a rayuwa, ta yadda gwamnati za ta iya tallafa musu a kungiyance.
Bayan an bude ta a Kaduna sai ya bayar da umarni a bude ta a sauran lardunan da ke Arewa. Zan iya cewa Jam’iyyar Matan Arewa gadarta na yi, domin mahaifiyata ita ma ’yar wannan kungiya ce. Tun muna yara muka tashi muka ga mahaifiyarmu tana harkar wannan kungiya. A wancan lokaci iyayenmu sun yi aiki a kungiyar inda suka bude ajujuwan yaki da jahilci ga mata kuma aka yi sa’a mazan suka ba mata kwarin gwiwa da goyon baya su kuma matan suka mayar da hankali. Haka kuma matan suka samu wayewa.
Gaskiya magabatanmu sun yi wa wannan kungiya hidima inda har suka bubbude rassan kungiyar a kauyuka hakan ya sa ta kawo har yanzu ana jin duriyarta.
A yanzu da na zama shugabar kungiyar a nan Kano muna nan muna koya wa mata sana’o’i yadda za su dogara da kansu. Mun lura mata yanzu sun fara sakankancewa sun daina sana’a suna jira mazansu su ba su. Muna ta kokarin jan hankalinsu don su samu sana’a. su kansu ’ya’yanmu matasa da suke karatu muna koya musu sana’o’in hannu yadda za su dogara da kansu su kuma kula da gidajensu.
Haka kuma muna yaki da harkar nan ta shaye-shayen miyagun kwayoyi musamman ma da ’ya’ya mata suka shiga ciki.
Baya ga koya musu sana’a mukan ba su tallafi daga dan abin da muke tarawa a junanmu, lokaci zuwalokaci.
Nasarori:
Alhamdulillah zan iya cewa nasarata a rayuwa ita ce yadda na san jama’a ni ma aka san ni. Ina kuma da alfarma a wurare da dama saboda mu’amalar da muka yi da jama’a daban-daban. Na biyu kuma ina jin dadi na bauta wa kasata.
Kalubale:
Ba za a ce mutumin da ya yi aiki a ce bai fuskanci kalubale ba, sai dai alhamdulillah duk kalubalen da ya zo Allah Yana kawo mafita a cikinsa.
Iyali:
Ina tare da maigidana da ’ya’yana uku, dukansu maza ne. Babban cikinsu yana da aure da ’ya’ya, na biyun yana jami’a sai kuma dan autana da yake shekarar karshe a sakandare.
Burina:
Babban burina shi ne in ga ina taimaka wa al’umma, don watakila ta wannan hanya mutum ya samu Aljanna. Ina kuma da burin in ga mata sun zama masu dogaro da kansu. Ina kuma so in ga matasa sun mike wajen neman na kansu.
Abin da nake so a tuna ni:
Ina so ko bayan raina a ce ga wata wacce ta yi kokari wajen canja rayuwar mata inda suka ginu suka samu wayewar kai.
Mutane abin koyi:
Akwai shugabannin da na yi aiki da su wato Dije Yahaya da A’ishatu Isma’il. Wadannan mutane jajirtattu ne ta fuskar ayyukansu. Ba su taba yarda jinsinsu ya sa sun gaza a aikinsu ba. Haka kuma tsayayyu ne a gidajensu domin dukansu duk da kasancewarsu ma’aikata su suke girka wa mazansu abinci da kansu, domin ita Dije har fura take daka wa mijinta da kanta. Haka kuma ba su bari aikinsu ya hana su ba ’ya’yansu tarbiyya ba.
Shawara ga mata:
Ina kira ga ’yan uwana mata mu yi hobbasa mu nemi na kanmu. Mu tuna addininmu bai bar mu kara-zube yadda za mu zama lusarai ba. Haka kuma ya kamata mu kula da tarbiyyar ’ya’yanmu. Kowace uwa da ta haifi danta tana son sa, amma hakan ba zai sa mu shagwaba yara ba. Nauyi ne a kanmu mu jajirce wajen tarbiyyar ’ya’yamu yadda gobe za mu yi alfahari da su. Akwai bukatar mu zama matan Musulmi abin koyi .