Hajiya Inna Mai Bukar Machina, ’yar marigayi Sarkin Machina a Jihar Yobe, ta yi Babbar Kwaminishina a Hukumar Kula da Harkokin Majalisar Dokokin Jihar Yobe. Tsohuwar Shugabar Makarantar Firamare, tsohuwar Shugabar riko ta Karamar Hukumar Machina, kwararriyar malamar makaranta ce da ta koyar na shekaru masu yawa kafin ta koma ofis a shekarar 2011, kuma ta yi ritaya. A zantawarta da Aminiya, ta bayyana tarihin rayuwarta da sauran bangarorin da suka shafe ta kamar haka:
Tarihin rayuwata:
Sunana Hajiya Inna Mai Bukar. Ni Kanuri ce daga Karamar Hukumar Machina a Jihar Yobe. Ni ’yar marigayi Sarkin Machina ne. An haife ni a garin Machina a ranar 17 ga Yulin 1958. Da na isa shiga makaranta sai aka sanya ni a makarantar firamare ta Central da ke Machina a 1964 zuwa 1970. Bayan na gama sai na tafi sakandaren al’umma wato Community Secondary School ta Nguru daga 1970 zuwa 1974 ban kammala a nan ba sai na tafi Kwalejin ’Yan mata ta Yola (GGC), da ke Yola a tsohuwar Jihar Gongola na kammala inda na yi GCE don a lokacin sababbin makarantun sakandare na al’umma din ba a tantance su ba. Na gama a 1975 daga nan sai na tafi Bauchi a wannan shekara ta 1975 zuwa 1976 na samu takardar shaidar malanta ta Pibotal. A 1977 sai aka yi mini aure. A 1979 na tafi Jami’ar Maiduguri na yi kwas a harshen Kanuri na shekara daya daga nan sai na zama Hedimastar Firamaren Hausari da ke Nguru a 1981 zuwa 1982, sai na tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na karanta fannin tattalin gida, daga nan na sake komawa Kwalejin Ilimi ta garin Gashuwa daga 1987 zuwa 1990 na yi NCE saboda in zama kwararriyar malama. Da na dawo a lokacin aka kirkiro da Karamar Hukumar Machina da Yusufari muka bar Nguru sai na zama Hedimastar makarantar Firamare ta Central a Kumagam. Ina nan sai aka mayar da ni bangaren mulki ina kula da sashin ilimin ’ya’ya mata daga nan sai aka ba ni Mataimakiyar Sakataren Ilimi ta 1. A wancan lokaci sai aka ware Machina daban Yusufari daban, kowacce tana zaman Karamar Hukuma mai ’yancin kanta sai a 1991 aka ba ni Sakatariyar Ilimi har zuwa 1999. Daga 1999 ne aka mayar da ni Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Yobe a matsayin Mataimakiyar Babbar Sakatare har zuwa 2001 daga nan sai aka mayar da ni Ma’aikatar Mata a matsayin Mataimakiyar Babban Sakatare. A 2003 sai aka aka kai ni Ma’aikatar Lafiya a wannan matsayi na Mataimakiyar Babbar Sakatare, ina nan sai a shekara ta 2005 zuwa 2006 aka ba ni Shugabar Rikon Kwarya ta Karamar Hukumar Machina inda na yi wata shida-shida sau biyu. Bayan nan a shekarar 2007 zuwa 2008 aka kai ni kula da ofishin shiyyar Legas wato Liaison office a lokacin babu Mataimakiyar Babban Sakatare. A shekarar 2009 zuwa 2010 na zama Daraktar Tsare-Tsare da Bincike da kuma Kididdiga a Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Yobe, a shekara ta 2011 na yi ritaya daga aiki.
Kalubale:
Kalubalen da na fuskanta shi ne a lokacin da nake Sakatariyar Ilimi na yi kokari an kai makarantar kwana ta mata a Machina wanda da babu ita amma bayan na bar wajen sai komai ya lalace ya koma baya. Na yi takaicin wannan shi ne ya sa nake jin haushin hakan a kullum, sannan wani abu da zan kira shi kalubale kasancewata mace ’yar sarauta ina aiki. Ga aure, ga kula da gida wani lokacin abubuwan suna yawa har ma ka rasa yaya za ka yi.
Nasarori:
Gaskiya babbar nasarata ita ce a lokacin da na zama sanadiyyar samun makarantar kwana aka watsar da ita da na dawo a matsayin shugabar rikon kwarya ta karamar hukumar na yi kokari na hada kai da gwamnati an sake farfado da makarantar har aka sake gina ta wasu suka kawo gudunmawar kwamfutoci da kayayyakin aiki wanda hakan ya yi matukar faranta mini rai. Sannan na samu nasarar ciyar da harkar ilimi gaba na zamani da na addini domin ina alfahari da yawan yaran da suka yi wannan makaranta ta kwana wadda da yawan su yanzu sun zama wadansu a Jihar Yobe da Najeriya, ni ne kuma na fara hada makarantar Islamiyya don a lokacin akwai ta Arabiyya amma babu ta Islamiyya. Na dinka wa yara yunifom da littattafan karatu a kauyuka da suke yankin Machina. A lokacin an samu yara sama da 200 suna zuwa Islamiyyar. Har ila yau a garin Machina sama da shekara 50 ana fama da wahalar ruwa ina zama shugabar riko na hada kai da kwararru aka wuce wurin. Sannan na wayar da kan al’ummar yankin wajen, musammam mata sanin muhimmancin katin zabe wanda a baya ba sa yi.
Lambay yabo:
A lokacin da na yi sanadiyar samar da makarantar kwana ta ’yan mata, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Yobe ta ba ni lambar yabo. Bayan da na yi kwas na Kanuri a Jami’ar Maiduguri, nan ma an ba ni lambar yabo. A lokacin da na yi NCE nan ma an ba ni lambar yabo na dalibar da ta zama zakara.
Hutu:
A lokacin da nake yin hutu ba na zuwa ko’ina ina yin hutu ne tare da iyalaina a gida, ba na zuwa wata kasa da sunan hutu, iyalaina nake bai wa lokacina.
Tufafi:
Nakan sanya sutura ce irin ta Kanuri wato zane da riga da dogon mayafi.
Burina:
Burina shi ne in wayar da kan al’umma musamman mazauna yankuna karkara da su san ’yancinsu saboda a wasu lokutan ana barinsu a baya.
Yawan iyali:
Alhamdulillahi, Allah Ya azurta ni da ’ya’ya takwas da jikoki 21.
Kasashe:
Na je Saudiyya aikin ibada sannan kuma ina zuwa Nijar da wasu kasashe a Afirka.
Shawara ga iyaye:
Shawarata ga iyaye shi ne su san ilimin ’ya mace yana da muhimmanci, saboda idan ’ya mace ta samu ilimi to za ta samu natsuwa na gudanar da komai nata cikin natsuwa ba tare da fuskantar matsalaloli ba. Haka tarbiyyar gida za ta sha bamban da wacce ba ta yi ilimin ba, sannan fa ko da wajen kula da maigida ne da sauran abubuwa na yau da kullum, idan tana da ilimi za ta yi su yadda ya dace. Iyaye ku gane dora wa ’ya mace talla ba alheri ba ne, domin tarbiyyar ’ya mace a wajen talla yake fara lalacewa. Idan uwa za ta yi jaurar sayarwa ba sai lailai ta dora wa yarinya ba, ta yi a gida za a rika zuwa ana saye amma idan ta ce sai ’yarta ta je talla ta gane ba gata take yi mata ba, kuma da ’yar da take talla da wacce ba ta talla akwai bambanci. Ita ’yar talla abin da take samu bai iya yaye musu talauci. Ga takaicin rayuwa, ga koyon rashin kunya kuma idan maganar tattalin kayan daki ne ke sa wadansu iyayen dora wa ’ya’ya talla abin da suke samu din bai ko iya saya musu abin da za su ci, balle kayan dakin.Don haka nake jan hankalin iyaye musammam mu mata mu gane talla illa ce ga ’ya’yanmu, don haka mu ba su dama su yi karatun addini da na zamani shi ne mafita. Da fatan Allah Ya shirya mana abin da muka bari.