✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in wakilci Najeriya a gasar daga nauyi ta duniya -Sulaiman Deni

Wakilin Aminiya Abubakar Haruna ya tattauna da wani matashi mai suna Sulainman Abdullahi  Deni wanda ya yi fice wajen wasan daga nauyi a Jihar Legas.…

Sulaiman Abdullahi Deni yana daga wasu karafuna. Wakilin Aminiya Abubakar Haruna ya tattauna da wani matashi mai suna Sulainman Abdullahi  Deni wanda ya yi fice wajen wasan daga nauyi a Jihar Legas. Saboda sha’awar wasan daga nauyi Sulaiman ya bude wurin daga nauyi don horar da jama’a masu sha’awa a Jihar Legas.

Jama’a za su so ka bayyana cikakken sunanka?
Sunana Sulaiman Abdullahi wanda ake yi wa lakabi da Deni. Duk wanda ka ce kana neman Deni a nan kasuwar Abbatuwa to zai kawo ka wurina. Babu wanda bai san ni ba a nan kasuwar. Ni dan asalin karamar Hukumar Dala ne a cikin Jihar Kano. Na sanya wa wannan wuri gidan Deni ne saboda Deni shi ne sunan da na yi fice da shi a nan Jihar Legas. Wasu da dama ma ba su san sunana na gaskiya ba sai Deni suka san ni da shi saboda da wuya ka ji wani ya kira ni da sunan Sulaiman.

Ka kai shekara nawa kana wasan daga nauyi?
A gaskiya na kai  shekara 13 amma kuma wani abin alfahari shi ne a tsawon shekarun da na yi ina wasan daga nauyi ban taba shan wata kwaya ba don na kara kuzari ko kuma don na kara girma. Wannan karfi da girman jiki da na samu tsabar daga nauyi ne yau da gobe.

Me ya ba ka sha’awa ka bude gidan wasan daga nauyi?
Abinda ya ba ni sha’awa shi ne don na samu kwarewa ta musamman a wasan daga nauyi. Kuma idan na sanya kaya su rika yi mini kyau a jiki sannan kuma na rika yi wa jama’a kwarjini. Don gaskiya idan kana daga nauyi babu wanda zai raina maka hankali kuma mutum duk rashin kunyarsa babu yadda za a yi ya yi maka rashin kunya, don ya san ka fi karfinsa.

Wane buri kake so ka cimma a wannan harka?
Burina shi ne na samu damar wakiltar kasata Najeriya a wasan daga nauyi na duniya. Ina so kuma na yi fice don a san ni a Najeriya da duniya baki daya. Shi ya sa na mayar da hankali akan harkar. Kuma nake bin ka’idojin wasan. Kuma ina da burin na rika shirya gasar daga nauyi amma rashin kudi  ke kawo mini tarnaki.
 
A kullum mutum nawa ne suke zuwa don daga karfe mai nauyi a wannan wuri?
Akalla mutum 15 suke zuwa suna koyon wasan daga nauyi. Akwai ’yan sanda da sojoji da ma’aikata da ’yan kasuwa. Akwai Hausawa da Yarabawa da kuma ’yan kabilar Ibo duk suna zuwa.

Wane alfanu ake samu a wasan daga nauyi?
To gaskiya akwai amfani don wadansu da dama daga cikinmu sun koma damben zamani wasu kuma sun koma kokawa ta zamani. Ni ma nan gaba kadan nake son komawa kokawa saboda na samu girman jikin da zan iya yin wasan kokawa.

Kukan kamu da ciwo sakamakon daga nauyi?
Ba a samun wani ciwo sai dai ma ka samu waraka daga wata cuta da take damunka kamar cutar maleriya da taifod da ciwon kai da zazzabi da shawara. Saboda haka ita wannan harka ta daga nauyi idan kana yi cuta ba za ta kama ka ba saboda magani ne na hakika. Idan kana yi za ka rika gumi da zufa. To wannan gumin da kake yi kana zubar da kwayoyin cututtukan da suke jikinka ne. Saboda haka idan kana daga nauyi babu ruwanka da shan maganin basur da  shawara da kuma maleriya.

Nawa kake karba idan mutum yana so ya yi rijista?
Nakan karbi Naira dubu daya kawai. Na bude wannan wuri ne don na taimakawa jama’a masu sha’awar wasan daga nauyi. Shi ya sa ba na takurawa. Wasu ma kyauta suke zuwa suna yi. Kuma ni kaina na taba rijista da hukumar wasanni tun ina Apapa da dadewa.