Hajiya Hauwa Bashar, tsohuwar malamar makaranta ce kuma kwararriyar Jami’ar kula da kiwon lafiya wacce bayan ta yi aikin malanta kuma ta canja layi zuwa aikin asibiti yanzu haka ta bude asibiti mai zaman kansa mai suna Yottere Maternity and Health Clinic. A zantawarta da Aminiya ta tabo tarihin rayuwarta kamar haka:
Tarihin rayuwata:
Sunana Hauwa Bashar, ni Bafulata ce gaba da baya. Ni ’yar asalin karamar Hukumar Akko ce a Jihar Gombe. An haife ni ne a Gombe a shekarar 1969. Na fara firamare tun shekaruna ba su kai shiga ba nake zuwa amma ba a yi mini rajista ba a firamaren da ke karamar Hukumar Akwanga a lokacin Nasarawa tana hade da Jihar Filato, amma da iyayena suka koma Legas a shekarar 1970 aka sa ni a ta ‘ya’yan sojoji wato Army Children School 3 Ikeja. Ban gama a can ba muka koma Gombe aka sa ni a firamare ta Central a nan na gama a shekarar 1980. Daga nan sai na ta fi sakandaren ’yan mata ta Women Teachers’ Collage Azare WTC daga 1981 zuwa 1986. Bayan na gama a shekarar 1988 sai aka yi mini aure a Gombe amma mijina yana aiki a Nabordo a Bauchi ba mu jima tare ba ya yi hatsari Allah Ya yi masa rasuwa a ranar 2 ga watan Disamba na 1988.
Aiki:
Na fara aiki ne da karamar Hukumar Akko a ma’aikatar ilimi a matsayin Malamar Makarantar firamare a Central ta Kumo a ranar 23 ga watan Janairu shekara ta 1989. Ina koyarwar a watan Satumba na 1989 sai na sayi fom na Kwalejin aikin ungozoma a Bauchi na tafi karatu har na gama na zama ungozoma, na gama a shekarar 1993. Da yake ina koyarwa ne na tafi karatu, da na dawo sai na koma wajen aikina sai suka tura ni asibitin karbar haihuwa na Kumo na yi shekara daya na sake komawa makarantar aikin jinya ta School of Nurse a garin Bauchi na yi Post Basic a bangaren jinya, na gama a shekarar 1996, sai na sake dawowa karamar hukumar sai suka sake tura ni garin Akko wato Akko billage a matsayin mataimakiyar shugabar asibitinsu. Ina nan a shekarar 1988 sai aka sake dawo da ni cikin garin Kumo a karamin asibitin yanki wato Primary Health Care a matsayin mataimakiyar babbar jami’ar asibitin, Deputy in charge, ina nan a wajen sai na nemi aiki a Ma’aikatar Kula da Lafiya ta Gwamnatin Tarayya, Federal Medical Centre (FMC) da ke Gombe wanda yanzu ya koma asibitin kwararru na gwamnatin tarayya Federal Teaching Hospital a shekara ta 2000, sai na samu amma ban tafi ba saboda lokacin samun karin girmana ya kusa sai kawaye na suka ba ni shawarar na zauna idan na samu karin girma ya fito sai na tafi. Hakan kuwa aka yi da karin girman ya fito sai na tafi a matsayin canjin wurin aiki wato Transfer of Serbice.
kalubale:
Gaskiya da nake aiki a karamar hukuma ban fuskanci kowannen irin kalubale ba saboda yadda nake tsara komai nawa. Ba na bari aikin gida ya rinjayi na ofis ko na ofis ya rinjayi na gida, sai dai da na zo tafiya asibitin koyarwa na tarayyar ne muka kusa mu samu matsala da mijina inda ya hana ni har sau biyu, na ukun ne ya bar ni da kyar. Shi ne na ce masa ya sani fa a karamar hukuma nake yanzu kuma zan koma gwamnatin tarayya ci gaba ne ya samu. Sai dai wani kalubalen da na fuskanta a Medical Center ne na yadda idan ’yan uwan marar lafiya suka taru a dakin jinya in ka ce su fita likita ya zo, sai wasu su gaya maka bakar magana.
Nasara:
Akwai nasara sosai domin duk aikin da na yi a asibiti ne kuma a dakin haihuwa wanda hakan ya ba ni dama ina gayawa mata matsalolin haihuwa da wasu ba sa gaya musu idan mace za ta haihu. Na farko ta kan tambayeni ya zafin haihuwa yake sai na gaya mata wanda hakan ya sa wasu suke jin dadin shawarar da nake ba su har muke saba wa da su.
Hutu:
A lokacin hutu ba na zuwa wani gari a Gombe nake hutu cikin ’yan uwa sai dai akwai wani lokaci da na kan je Kaduna wajen wani wana nake yin hutu tare da iyalansa.
Tufafi:
Ni a matsayina na ’yar Arewa na fi sha’awar zani da riga da babban gyale, wanda duk ya gan ni da shi ya san ya rufe mini jiki.
Burina a rayuwa:
Burina shi ne in ga a kowanne lokaci na taimaki marar karfi a rayuwa musamman a bangaren ilimi don idan mutum ya samu ilimi shi ne zai samu madogara a rayuwar sa.
Yawan iyali:
Alhamdulillahi ina da ’ya’ya 6, uku maza, uku mata, kuma ina kula da su daidai gwargwado a bangaren iliminsu da tarbiyyar su.
Shawara ga iyaye:
Ina mai bai wa iyaye shawara kan su sani karatun ’ya mace yana da muhimmanci, don idan mace ta yi karatu ta samu ilimi tarbiyyarta za ta zama daban da wacce ba ta da ilimi. Kuma ilimin ya zama na addini da na boko. Sannan idan mace ta yi ilimi za ka ga ’ya’yanta za su samu tarbiyyar fiye da ’ya’yan wacce ba ta da ilimi, kuma hatta ’ya’yan makwabta za su amfana da ilimin ta. Sannan ina mai yin kira ga iyaye a daina dora wa ’ya’ya mata talla, don tallan ’ya mace ba alheri. Kai namiji ma bai kamata ya yi talla ba balle mace.