✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in taimaka wa mabukata – Barista Khadijatu Abdullahi Adamu

Barista Khadijatu Abdullahi Adamu ita ce uwargidan tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu. Yanzu haka mijinta ne Sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu…

Barista Khadijatu Abdullahi Adamu ita ce uwargidan tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu. Yanzu haka mijinta ne Sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa. Sannan ita ce Manajan Otel din Keffi Hotel. A tattaunawarta da wakilinmu ta bayyana tarihin rayuwarta da batutuwan da suka shafi mata da sauran bayanai kamar haka:

Tarihinta
Sunana Barista Khadijatu Abudullahi Adamu. Na yi karatun firamare a Kara Primary School da ke Patiskum a Jihar Yobe a shekarar 1976 inda na kammala a shekarar 1981. Daga nan na cigaba a sakandaren mata zalla ita ma a Patiskum daga shekarar 1981 zuwa 1986. Daga nan na cigaba da karatu a a Jami’ar Maiduguri inda na samu difloma a fannin shari’a  (Shari’a Law) inda na kammala a shekarar 1988. Bayan na samu digiri  a jami’ar sai na cigaba da yin karatun Lauya a Makarantar Lauyoyi ta Legas a shekarar 1993. A wannan shekara ce na yi aure watau 1993. Daga nan na yi bautar kasa a ma’aikatar shari’a da ke garin Jos a Jihar Filato a shekarar 1994. Kadan daga cikin tarihina kenan.

Halayen da na koya a wajen iyayena:
Iyayena sun koya min kyakkyawan tarbiyya a lokacin da nake tare da su da ba zan taba manta wa ba. Ka ga musamman batun rike addini, iyayena sun koya min wannan sosai. Mutane ne da ke son bauta wa Allah,  shi ya sa suka koya mana mu ‘ya’yansu wannan sosai. Sun koya mana guje wa duk wani halin da ya saba wa addinin Musulunci akoyaushe. Haka kuma iyayena sun koya min halin zamantakewa wato yadda za mu zauna da makwabta da sauran jama’a da muke hulda da su lafiya ba tare da mu nsamu matsala da su ba. Misali, a gidanmu dole ne ka girmama na gaba da kai, ko ka san shi, ko ba ka san shi ba. Muddin ya girmeka ya zame maka dole ka ba shi wannan girma. Saboda haka a takaice na samu kyakkyawar tarbiyya daga wurin iyayena a lokacin da nake tare da su da idan na ce zan bayyana su za mu dade ban kare ba. Abin da nake musu yanzu shi ne addu’ar Allah Ya saka musu da alheri kuma ba zan taba mantawa da su ba.

Nasarorin da na cimma a rayuwata:
Bari in fara da bangaren karatu. A gaskiya ba wai alfahari ko wani abu makamancin haka ba, zan iya cewa na samu gagarumar nasara a bangaren neman ilimi don na san abin da nake fadi. Haka a bangaren aure. shi ma babban nasara ce don kamar yadda ka sani da ikon Allah na auri daya daga cikin wadanda idan ana maganar siyasa a Jihar Nasarawa dole ne a ambaci sunansa. Allah Ya ba shi mukamin jagorancin al’ummar jihar nan har na tsawon shekaru 8 sannan a yau kuma Sanata ne. Saboda haka ba alfahari ba zan ce na samu nasara a wannan bangare. Don mai gidana mutum ne da ya san mutuncin aure duk da cewa dan siyasa ne. Yana kulawa da iyalansa daidai da yadda addinin Musulunci ya tanadar wanda hakan ya sa ban taba samun matsala da shi ba a tsawon lokaci nan da muke tare. Haka kuma Allah Ya albarkace ni da ‘ya’ya. Kadan daga cikin abubuwa da zan iya ce na samu nasara akansu kenan.

kungiyoyin da nake ciki:
Daga cikin kungiyoyi da nake ciki akwai wata kungiya da ake kira Afo Debelopment Association, ni membar kungiyar ce. Akwai kuma kungiyar mata masu yin wa’azin Musulunci  da ake kira Women in Da’awa, da kungiyar matan musulmi da akafi sani da FOMWAN wanda ni mamba ce a kungiyar, da dai sauransu. Ina so in yi amfani da wannan dama in sanar da kai cewa ina da tawa kungiyar da na kafa a lokacin da maigidana ke Gwamnan Jihar Nasarawa, wannan kungiya ana kiranta kungiyar kwato wa mata da yara ’yanci.  Kungiya ce da ke taimaka wa yara da mata musamman marayu da sauransu. Na ga ya dace ne in kafa wannan kungiyar bayan na yi la’akari da yadda mata da yara musamman wadanda suka rasa mazajensu da kuma marayu suna cikin mawuyacin hali. Shi ya sa na kafa wannan kungiya wanda a yau Alhamdullilah da yardar Allah zan iya cewa mun cimma burinmu na kafa wannan kungiya.
kalubalen da nake fuskanta a rayuwa:
kalubalen dai bai wuce na kulawa da yara da jama’a ba. Kamar yadda ka sani maigidana sananen dan siyasa ne da hakan ya sa akoyaushe muke tare da jama’a. Ba na ma ganin haka a matsayin kalubale don a matsayinka na shugaban jama’a dole ne ka bauta musu wato ka yi iya kokarinka wajen biya musu bukatu daidai gwargwado. Wannan shi ne abin da ake nufi da shugabanci.  
Abin da zan so a tunani da shi:
A gaskiya zan so a tuna da ni akan yadda nake kulawa da yara da mata ta kungiyata da na bayyana maka. Idan za a ce ai wace ta taimaka wa marayu da mata da dama a bangaren karatunsu da lafiyarsu da sauransu a gaskiya hakan ya ishe ne don shi ne babban burina a rayuwa. Dole a taimakawa wadannan mutane don mutane ne dake matukar bukatar taimako. Saboda haka a takaice ina so a tuna da ni a matsayin wace ta tallafa wa mata da yara da marayu da sauransu.
Shawarata ga mata:
Shawarar ita ce mata su kula da karatun ‘ya’yansu. Haka mu kanmu mu tabbatar mun nemi ilimi don shi ne zai taimaka wa mace a rayuwar yau. Idan mace ba ta samu damar karatu ba sai ta kama sana’a don hakan zai taimaka mata zai kuma taimaka wa al’umma baki daya. Nagode.