✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in sauya rayuwar mata ta hanyar shirye-shirye a gidan rediyo – Saratu Musa Hadeja

Cikakken sunanta: Sunana Hajiya Saratu Musa Hadeja daya daga cikin Daraktocin gidan radiyon Jihar Jigawa kuma babbar daraka mai kula da adana bayanai a gidan…

Cikakken sunanta:

Sunana Hajiya Saratu Musa Hadeja daya daga cikin Daraktocin gidan radiyon Jihar Jigawa kuma babbar daraka mai kula da adana bayanai a gidan rediyon Jihar Jigawa.

Tarihina:

An haife ni a garin Hadeja da ke Jihar Jigawa a areawacin Najeriya.   An haife ni a shekarar 1963.   Na yi karatun firamare a garin hadeja a makarantar da ake kira Abdulkadir Primary School sannan na yi karatun sakandare a Kwalejin ’yan mata ta Shekara da kuma Kwalejin WTC da ke Gezawa, amma saboda a lokacin ba a kammala gininta ta ba a Goron Dutse muka ci gaba da daukar karatu sai dai muna daf da kammala ne aka kammala ginin makarantar inda aka mayar da mu can muka kammala a Gezawa.

Sannan a nan na fara aikin koyarwa a WTC bayan da na kammala karatun sakandare aka dauke ni aiki a matsayin malama na rika koyarwa a lokacin ina da takardar shaidar karatu ta malanta mai daraja ta biyu wato Grade II.

Bayan wani lokaci ina aikin koyarwa sai na koma karatu a Arabic Teachers Collge  (ATC/ABU) a lokacin muna Jihar Kano wanda yanzu ita ce Kwalejin Horar da Malamai  (FCE).   Na gama karatun NCE aka tura ni Sakkwato yin bautar kasa a shekarar 1984.   Na yi aikin koyarwa a Kwalejin Giginya Barak a lokacin da na yi bautar kasar a Sakkwato har sun nemi su rike ni na yi masu aikin koyarwa  amma ban amince ba saboda wasu dalilai.

Bayan na dawo gida aka dauke ni aiki aka turani Kwalejin ’yan mata ta Birniwa a 1985 zuwa 1986 daga nan ne aka yi mini aure.  Kasancewar ni kadai ce mace a makaranatar sai na zama tamkar ni ce mataimakaiyar shugabar makarantar saboda ni ce nake taimako wajen tafiyar da harkokin makarantar.   Na sha wahala kafin a sauya mini wurin aiki ni da mijina a wancan lokacin saboda mijina na farko ma’aikaci ne a kamfanin jirgin sama na Kabo da ke Kano aka kiransa da suna Abdulhadi Yunusa Kafin Hausa amma tuni Allah Ya yi masa rasuwa amma daga baya sai na auri mijina na yanzu wato Kwamared Mohammed Garba Malam Madori da shi ma yake aiki a Gidan Rediyon Jihar Jigawa.  Har yanzu muna tare da shi. Daga nan ne aka yi mini sauyin makaranta na koma wata makaranta da ake kira sakandaren  Paybotal da ke Kano a Goron Dutse a 1985.   Ina can ne na koma karatu a Jami’ar BUK a 1989 inda na yi digirina na farko a bangaran ilimi wato (BA. EDUC).  Bayan na kammala karatun digiri a 1991sai na koma koyarwa a makarantar da nake aiki wato Paybotal a matsayin malama.

Amma a lokacin da aka kirkiro Jihar Jigawa sai na yi sha’awar na koma gida sai aka turani Kwalejin ’yan mata ta Malam Madori na cigaba da aikin koyarwa. Bayan an bude gidan rediyon Jihar Jigawa da yake ina da sha’awar aikin jarida kuma a lokacin ana bukatar masu yin fasara da yake Hausa na karanta sia na rubuta takardar neman aiki aka dauke ni a shekarar 1993.   Na fara aiki a bangaren aiwatar da shirye shirye na gidan radiyon.   Ni ce na fara aiwatar da shirin mata hasken gida, wani shiri ne kamar hatsin bara wanda ya kunshi abubuwa daban-daban da ya shafi al’umma. 

Sannan ni ce ke aiwatar da shirin filin yara da kuma shirin Kids Help Our Futures  da shirin Future Leaders na turanci da kuma shirin Ku Taho Yara na Hausa.  Wannan shirin ya taimakawa yara wajen bayyana ra’ayoyinsu da burinsu a lokacin da suke yara kuma da dama wadanda na yi shirin da su burinsu ya cika domin sun zama abin da suke bukatar su zama.   Wasu suna da burin zama likitoci kuma sun zama wasu na da burin zama lauyoyi sun zama.   Wasu na da burin zama malaman makaranta kuma sun zama.

Saboda sha’awata wajen inganta harkokin jama’a a Jihar Jigawa na sanya kaina cikin harkokin kungiyoyi da dama kamar su DFID da UNICEF da AIDS CAPS da WHO da sauransu.   Haka kuma na yi hulda da kungiyar FOMWAN har na rike mukamin Amira na tsawon shekara 11. Kuma na yi PRO na kungiyar tsawon shekara 3.   Sannan na yi aiki da kungiyar Raya Ilimi a Karkara a lokacin Hajiya Zahara’u Saminu Turaki ita ce ke shugabantar kungiyar a Jihar Jigawa, amma a yanzu Hajiya Habiba Isah Gambo Dutse ce ke wakiltar Hajiya Zahara’u Saminu Turaki a matsayin shugabar kungiyar.  Sannan mu ne muka kafa kungiyar Mata Masu Da’awa a Jihar Jigawa domin fadakar da mata yadda za su ghudanar da harkokin zamantakewar aure da inganta harkokin ibada kuma mun kafa ofisoshinmu a daukacin kananan hukumomi 27 na Jihar da nufin fadakar da mata yadda za su gudanar da harkokin addini domin wallahi a wasu kauyukan mun sami mata ba su san yadda za su yi wankan haila da na janaba ba.  Sannan ba su san a rama azumi idan an sha ba saboda jahilci.

Mukaman da ta rike a gidan Rediyon Jihar Jigawa:

Na taba zama shugabar tashar Andaza FM wacce karamar tasha ce dake Andaza a jahar Jigawa yanzu haka ni ce shugaba wato Darakta a sashen adana bayanai da bincike agidan radiyon Jigawa.  Sannan na rike mukamin Darakta a sashen yada labarai har na  tsawon shekara 2.  A halin yanzu ina kula da ofisoshi biyu ne da ke karkashina a gidan rediyon Jihar Jigawa.

Burinta a rayuwa:

Burina a halin yanzu shi ne in ga komai yana tafiya daidai wajen aiwatar da shirye shirye da nake gudanarwa a gidan radiyo.  Ina da burin in sauya rayuwar al’umma musamman mata ta hanyar shirye-shiryen da muke gabatarwa.

Gudunmawar da ta bai wa mata:

Na bai wa  mata gudunmawa ta hanyar bude cibiyar koyar da mata sana’o’in hannu yanzu haka da yawa daga cikinsu sun zama masu dogaro da kansu.  Sannan wadanda suka koyi sana’ar nakan ba su jari inda suke bude nasu na kashin kansu don su ma su koyar da wasu.  Yanzu haka ina yaye daliban da suka koyi sana’a a duk wata uku musamman a bangaren koyon dinki yara mai kama da na kanti (Ready made).

Makarantar da ta bude:

Wannan yana daga cikin burina, don yanzu haka na bude wata makarantar boko domin jama’a su amfana. Na bude makarantar ce a Unguwar Takur inda na fara da dalibai 6.  Bayan daliban sun karu da 38 ne sai na yanke shawarar kama hayar wani gida.  Da dalibai suka kara yawa ne sai na sayi wani fili a kan Naira dubu 250 a lokacin Gwamna Sule Lamido.  Yanzu haka na gina ajujuwa 12 da ofoshin malamai da ofishin shugaban makaranta da dakin karatu da aikin adana kaya wato Store.  Gaskiya yanzu haka makarantar ta fara zama da gidinta.

Yaya batun tsadar kudin makaranta a wajenki?

A gaskiya ban bude wannan makaranta don neman kudi ba, na bude ta ne kawai don in taimaki al’umma musamman ’ya’yan talakawa.  Duk fadin Jihar Jigawa babu makarantar da ta kai tawa sauki don muna karbar dubu 5 ne kacal a zangon karatu.  Yanzu muna da dalibai 280 da malamai 21 da leburori 7 da hakan ta sa jama’a ke rububin kai ’ya’yansu makarantar mu.

kasashen da ta taba ziyarta:

Na ziyarci kasashen Uganda da Nijar da Ingila a karkashin kungiyar FOMWAN don mu gano yadda mutane suke gudanar da harkar kiwon lafiya a wadannan kasashe da kuka yadda ake kula da ciwon sida.

Kasahe nawa kika ziyarta arayuwarki?

Banyi yawon duniya da yawaba na je kasashen Uganda da Nijar da Ingila a karkashin kungiyar FOMWAN domin mu gano yadda mutane suke gudanar da kiwon lafiya a wadancan kasashe da yadda ake kula da ciwon sida. 

Batun iyali:

Ina da aure da yara biyar